Gwamna Ya Lissafa Dalilan da za Su Sanya Talaka Zaben Tinubu a 2027

Gwamna Ya Lissafa Dalilan da za Su Sanya Talaka Zaben Tinubu a 2027

  • Gwamnan Kaduna, Uba Sani, ya ce Shugaba Bola Tinubu zai lashe zaben 2027 domin ci gaba da wa’adi na biyu
  • Uba Sani ya bayyana haka ne yayin taron maraba da tsofaffin jiga-jigan siyasa da suka koma jam’iyyar APC a Kaduna
  • Gwamnan ya ce jam'iyyar APC ta zama jam’iyyar da ke da karbuwa a Kaduna, Arewa da ma Najeriya baki daya
  • Wani matashi ya tattauna da Legit kan maganganun da gwamna Uba Sani ya yi a kan nasarar APC a zaben 2027

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kaduna - Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, ya nuna kwarin gwiwar cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai lashe zaben 2027.

Gwamnan ya ce ‘yan Najeriya za su sake zabensa saboda irin ayyukan ci gaban da yake yi a mulkinsa.

Kara karanta wannan

"Za mu kawo karshen mulkin kama karya," PDP ta musanta baraka a cikinta

Bola Tinubu
Gwamnan Kaduna ya ce Bola Tinubu zai lashe zabe a 2027. Hoto: Uba Sani|Bayo Onanuga
Asali: Twitter

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa gwamnan ya yi furucin ne yayin taron maraba da sababbin 'yan siyasa da suka koma jam’iyyar APC.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu zai ci zaben 2027 - Uba Sani

Gwamna Uba Sani ya ce babu tantama Shugaba Bola Tinubu zai sake lashe zaben 2027 don ci gaba da wa’adi na biyu.

Uba Sani ya bayyana cewa APC za ta yi nasara a dukkan matakan zabe, daga shugaban kasa har zuwa ‘yan majalisa.

Ya ce al’ummar Najeriya za su sake jefa kuri’a ga jam’iyyar APC saboda yadda take tafiyar da shugabanci cikin adalci.

Gwamnan ya kara da cewa a yanzu haka APC ce jam’iyyar da ke da karbuwa a Kaduna, Arewa da Najeriya baki daya.

Wadanda aka karba zuwa APC

Gwamnan ya tabbatar wa da sababbin ‘yan jam’iyyar cewa za su samu kulawa da dama kamar sauran tsofaffin mambobin APC.

Kara karanta wannan

Siyasa: Sule Lamido ya yi zazzafar nasiha ga malaman Izala da Darika

Ya ce wanda ya shiga jam’iyyar a yau da wadanda suka kafa ta shekaru 10 da suka wuce duk matsayinsu daya.

Taron dai ya samu halartar manyan ‘yan siyasa da suka dawo APC, ciki har da tsohon gwamnan Kaduna, Ramalan Yero.

Haka kuma Sanata Shehu Sani, Sanata Suleiman Hunkuyi da Sanata Danjuma La’ah sun halarci taron domin komawa jam’iyyar APC.

Uba Sani ya ce APC na karbuwa

Gwamna Sani ya ce jam’iyyar APC na samun karbuwa saboda adalci da shugabancinta ke gudanarwa.

Ya ce a shirye jam’iyyar take don karbar karin ‘yan siyasa daga jam’iyyu daban-daban kafin babban zaben 2027.

Ya kuma bukaci ‘yan Najeriya da su ci gaba da yi wa shugabanni nasiha ta hanyoyin da suka dace domin ci gaba da inganta harkokin shugabanci.

Haka zalika, ya jaddada cewa akwai bukatar hadin kai da goyon bayan jama’a domin tabbatar da nasarar APC a gaba.

Kara karanta wannan

APC ta yi raddi ga Tambuwal, ta fadi dalilin raba garinsa da jam'iyyar

An yaba da karfin APC a Kaduna

A yayin taron, tsohon sakataren gwamnatin jihar Kaduna, Samaila Yakawada, ya ce babu mai iya karawa da APC a Kaduna a 2027.

Ya bukaci duk masu shirin tsayawa takarar gwamna da su janye kudirinsu, yana mai cewa APC za ta ci gaba da mulki a jihar.

Legit ta tattauna da matashi a Kaduna

Wani matashi a jihar Kaduna, Muhammad Adamu ya bayyanawa Legit cewa har yanzu ba za a iya cewa ga wanda zai yi nasara ba a 2027.

Matashin ya ce:

"Idan aka lura da abubuwan da suke faruwa na saukar farashi a kwanakin nan, za a iya cewa APC za ta dawo da karfinta a 2027.
"Hakan zai sa babu tabbas kan hasashen zaben 2027. Amma idan aka cigaba da shan wahala, to dole APC za ta fuskanci kalubale babba a fadin Najeriya."

Dogara ya ba Tinubu shawari kan 2027

Kara karanta wannan

Shugabannin Arewa sun yiwa Ganduje kaca kaca, sun kalubalanci tazarcen Tinubu

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon shugaban majalisar wakilai, Hon. Yakubu Dogara ya ba Tinubu shawara kan sammun nasara a 2027.

Yakubu Dogara ya ambaci ayyukan cigaba da zai yi a jihar Bauchi domin shawo kan jama'a su sake zabensa cikin sauki domin yin wa'adi na biyu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng