2027: Atiku Ya Shirya Tafiya da Matasa, Ya Nada Tsohon Hadimin Gwamna Mukami

2027: Atiku Ya Shirya Tafiya da Matasa, Ya Nada Tsohon Hadimin Gwamna Mukami

  • Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya nada sabon mataimaki na musamman kan matasa da tsare-tsare
  • Atiku ya nada Tanimu Tahir ne wanda ya taba rike muƙamin hadimi na musamman ga Gwamna Babagana Zulum
  • Tanimu zai jagoranci dabarun shiga tsakani tare da matasa ta amfani da kafafen zamani da tarukan al'umma domin kamfen din Atiku na 2027
  • Wannan nadin na nufin kara karfafa matasa su zama masu tasiri a siyasa, tare da hada kai da kungiyoyin matasa da masu hangen nesa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Yola, Adamawa - Dan takarar shugaban kasa a zaben 2023, Atiku Abubakar ya yi sabon nadin mataimaki kan harkokin matasa.

Atiku ya nada Tahir Tanimu Tahir a matsayin mataimaki na musamman kan matasa da tsare-tsare.

Atiku ya nada matashi mukami domin shirye-shiryen zaɓen 2027
Atiku Abubakar ya nada tsohon hadimin Gwamna Babagana Zulum mukami domin siyasar 2027. Hoto: Atiku Abubakar, Tanimu Tahir.
Asali: Facebook

2027: Atiku ya nada matashi mukami a tafiyarsa

Kara karanta wannan

Mutuwar mutane a hadarin Kano ya girgiza jama'a, Sanata Barau ya yi ta'aziyya

Wasikar nadin da Leadership ta gani a Maiduguri ta bayyana Tanimu a matsayin kwararre mai kuzari da dabarun bunkasa matasa da sadarwa ta zamani.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tanimu ya fito ne daga garin Marama, a karamar hukumar Hawul a jihar Borno, a baya ya yi aiki a matsayin mataimaki na musamman kan harkokin rediyo a wa’adin farko na Gwamna Babagana Zulum.

"Tanimu na da sama da shekaru goma na kwarewa a harkokin bunkasa matasa, shiga tsakani a siyasa, dabarun kamfen, da hulda da kafafen watsa labarai."
"Nadinsa na nuna jajircewar Atiku wajen tabbatar da cewa an saka muradun matasa a cikin tattaunawar kasa ta hanyar tsare-tsare masu tasiri."

- Cewar sanarwar

A matsayin mataimaki na musamman, Tanimu zai jagoranci shirye-shirye na musamman domin hada Atiku Abubakar da matasa masu kuzari a Najeriya.

Za a mayar da hankali kan dabarun jawo hankalin matasa ta amfani da kafafen zamani, gwagwarmaya a matakin kasa, da tarukan al’umma.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta bayyana shirinta a kan ma'aikata a Najeriya

Matashin ya yi godiya bayan samun muƙamin

Haka kuma, Tanimu zai jagoranci yakin neman goyon bayan jama’a don kara haskaka hangen nesan Atiku na cigaban kasa ta hanyar matasa.

Tanimu ya godewa Atiku bisa wannan dama, yana mai cewa, Burimsa shi ne tabbatar da cewa muradun matasa sun samu karbuwa.

Ya kara da cewa wannan nadin zai taimaka wajen gina wani gagarumin kamfen na matasa domin cimma burin zabukan 2027.

Atiku ya jajanta da mutuwar Malamin Musulunci

Kun ji cewa Atiku Abubakar ya yi jimamin mutuwar babban malamin Musulunci a Adamawa, Sheikh Ibrahim Abubakar Daware.

Atiku ya yi ta'aziyyar bayan mutuwar Sheikh Daware wanda ya ba da gudunmawa sosai a rayuwarsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.