‘Arewa ba Za Ta Yafe ba’: An Fadi Yadda Tinubu Zai Lallabi Yankin a Zaben 2027
- Tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal ya ce idan Tinubu bai sasanta da Arewa ba, zai fuskanci barazanar rashin nasara a zaben 2027
- Lawal ya zargi manufofin Tinubu da jefa Arewa cikin kunci, yana kira ga shugaba ya saurari koke-koken al'umma
- Ya ce idan Arewa ta yanke shawara kan yadda za ta yi zabe a babban zabe, ba za a iya canza sakamakon ba
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babachir Lawal ya gargadi Bola Tinubu kan zaben 2027.
Lawal ya ce idan Shugaba Bola Tinubu bai gyara manufofinsa da neman yafiyar Arewa ba, yana iya rasa damar sake komawa kan mulki a zaben 2027.

Asali: Twitter
Jigon APC ya gargadi Tinubu kan zaben 2027
A wata tattaunawa ta musamman da Punch ta bibiya, Babachir Lawal ya ce Arewa ba za ta yafe wa Tinubu ba kan yadda ya jefa yankin cikin kunci ta hanyar manufofinsa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce Tinubu ya kawo wasu tsare-tsare da suka jefa yankin Arewa cikin wani mummunan hali.
Babachir Lawal wanda ya taba kasancewa aminin Tinubu amma yanzu sun samu sabani ya ce:
“Ya kamata ya gudanar da shirin da zai rage talauci a kasa, ba batun shi ba ne, batun manufofinsa ne.
"Suna jefa kowa cikin kunci, musamman Arewa, ya kamata ya gyara manufofinsa, ya saurari jama’a.”
'Abin ka iya faruwa a 2027' - Babachir Lawal
Babachir ya kuma zargi gwamnatin Tinubu da kame matasan Arewa da ke sukar manufofinsa, yana cewa an mayar da sukar gwamnati tamkar laifi a Arewa.
Da aka tambaye shi game da barazanar yi wa Tinubu abin da aka yi wa Goodluck Jonathan a 2015, Lawal ya ce idan Arewa ta dauki matsaya kan yadda za ta zabi, ba za a iya sauya sakamakon ba ko da da kudi.

Kara karanta wannan
'Abin da ya sa Tinubu zai ci zaben 2027': Kwankwaso ya magantu, ya tabo maganar Ganduje
Ya ce:
“A zaben Jonathan, an kashe kudi sosai amma mutane sun karba suka ki fita kada kuri’a, hakan na iya faruwa a 2027 idan Tinubu bai gyara ba.”
'Yadda Arewa za ta yaki Tinubu' - Babachir Lawal
A wani labarin, Babachir Lawal, tsohon sakataren gwamnatin tarayya, ya ce kiristocin Arewa za su yi amfani da addu'a da katin zabe don yakar tikitin Musulmi da Musulmi.
Jigon na APC ya ce akwai wata makarkashiya a jam'iyyar ta APC na yunkurin murkushe kiristocin Arewacin Najeriya amma ba za su bari ba.
Asali: Legit.ng