APC Ta Shawarci El Rufa'i a Kawo Ƙarshen Takun Saka da Gwamnatin Tinubu
- APC ta Kano ta tabbatar da tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa’i, ya bayar da gudunmawa a nasarar Bola Ahmed Tinubu a zaben 2023
- Wannan na zuwa ne duk da rashin jituwar da ke tsakanin tsohon gwamnan da gwamnatin tarayya, har ya ke ganin ana barazanar cafke shi
- Sakataren yada labaran APC na Kano, Ahmed S Aruwan ya shaida wa Legit cewa lokaci ya yi da El-Rufa’i zai tuna matsayinsa don yin sulhu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano — Jam'iyyar APC ta tabbatar da cewa tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa'i ya bayar da gudunmawa wajen samar da nasarar shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a zaben 2023.
Sakataren yada labaran APC, Ahmed S Aruwan da ya bayyana hakan ga Legit, ya kara da cewa ba sa jin dadin takun saka da ya shiga tsakanin tsohon gwamnan da gwamnatin tarayya.

Asali: Facebook
Kakakin jam'iyyar yake cewa amma wannan ba ya nufin suna goyon bayan yadda El-Rufa'i ke kokarin tadiye APC ta cikin gida, domin za a iya magance dukkanin koken da ya ke da su a cikin ruwan sanyi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An yi hasashen matsalar Nasir El-Rufa'i da APC
Ahmad Aruwan ya bayyana cewa bai cika son magana a kan tsohon gwamnan Kaduna, El-Rufa'i ba, ganin cewa har yanzu ba a gama tantance menene damuwarsa da jam'iyya ba.
Ya bayyana cewa:
"Na san da an kai sunansa a matsayin wanda za a yi wa Minista, daga karshe aka zo aka janye. Mai yiwuwa ba ya rasa nasaba da siyasarsu a Kaduna. Ba ya rasa nasaba da gwamnatinsu ta Kaduna da wanda ya gaje shi.
Wata rigimar daga cikin gida ta ke, daga gidanka ne za a tadiye ka, daga gidanka ne za a ce ba a sonka, daga gidanka ne za a yi maka bita da kulli idan ma ita ce.

Kara karanta wannan
"Tinubu zai sha wahala": LP ta bayyana wanda za ta tsayar takarar shugaban ƙasa a 2027
APC ta nemi El-Rufa'i ya zauna da Tinubu
APC ta tunatar da Nasir El-Rufa'i matsayinsa a siyasar Najeriya, da yadda ya taka rawa wajen samun nasarar jam'iyyar, tun daga lokacin Muhammadu Buhari zuwa Bola Tinubu.
Ahmed S Aruwan ya ce:
"Sai ka yi hakuri, sai ka zauna da jam'iyyarka, idan ma akwai matsala zai iya ganin shugaban kasa, zai iya ganin shugaban jam'iyya, a duba lamarin. Menene ya faru? Me ake ciki? Menene matsalarmu? Me mu ka yi? Menene laifin mu?
Ya kara da cewa da El-Rufa'i aka gina APC, saboda haka ya yi hakuri wajen neman a yi sulhun siyasa da jam'iyyar APC, domin ba za a iya goge tarihinsa a jam'iyyar ba.
El-Rufa'i ya yi magana kan shirin kama shi
A baya, mun ruwaito cewa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i ya bayyana cewa ba tun yanzu ya ke samun labarin cewa gwamnatin tarayya na shirin cafke shi ba saboda adawa da ita.
El-Rufa'i ya ce amma wannan barazanar ba za ta ba shi tsoro ba, ganin cewa shi dan gwagwarmaya ne a siyasa da ya dade ya na fuskantar makamancin wannan barazana daga gwamnatocin baya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng