"Kwankwaso na Kamun Kafa don Dawo wa Jam'iyyarmu," APC ba Ta Bukatar Jagoran NNPP

"Kwankwaso na Kamun Kafa don Dawo wa Jam'iyyarmu," APC ba Ta Bukatar Jagoran NNPP

  • Jam’iyyar APC ta bayyana cewa ba ta bukatar tsohon dan takarar shugaban kasa, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya koma jam’iyyar
  • Sakataren yada labaran APC na Kano, Ahmed S Aruwan ne ya shaida wa Legit haka, inda ya yi zargin babu abin da Kwankwaso zai kawo masu
  • Ya kara da cewa Kwankwaso ba shi da yawan magoya bayan da zai sa su ji tsohon sake kara wa da shi a babban zaben 2027 mai zuwa

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar KanoJam'iyyar APC ta bayyana cewa ta samu labarin yadda tsohon dan takarar shugaban kasa, Rabi'u Musa Kwankwaso ke kokarin koma wa jam'iyyarsu.

Sakataren yada labaran APC a Kano, Ahmed S Aruwan ne ya bayyana haka, inda ya ce ba sa bukatar Sanata Kwankwaso ya shiga jam'iyyar.

Kara karanta wannan

APC ta shawarci El-Rufa'i a kawo ƙarshen takun saka da gwamnatin Tinubu

Kwankwaso
APC ta ce ba ta neman Sanata Kwankwaso Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso/Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR
Asali: Facebook

A wani labari da ya kebanta da Legit, S Aruwan ya kafe a kan cewa shigar Kwankwaso APC ba zai jawo komai ba illa birkita jam'iyya, kuma ba sa bukatar hakan a yanzu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

APC: "Mun ji labarin aniyar Kwankwaso"

Ahmed S Aruwan, wanda shi ne ke magana da yawun APC a Kano ya ce a jam'iyyance, babu wanda ya sanar da su shirin cewa Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso zai koma jam'iyyar.

Amma ya ce sun samu labarin yadda ya ke ta fafutuka domin ya samu hanyar shiga APC, lamarin da Aruwan ke ganin ba zai yiwu ba.

Ya ce:

""Mu dai a matsayinmu na jam'iyya, zuwa yanzu din nan, ba wanda ya yi mana magana, ba mu san da maganar ba.
"Kuma ina so in tabbatar miki da cewa mu ba ma gayyatar rigima, ba mu neman fitina."
"Bukatarmu ita ce mu samu zabe, mu ci zaben 2027, mai girma shugaban kasa, Tinubu ya ci zabensa, ba tare da gardama ba."

Kara karanta wannan

Yadda Kwankwaso ya fara gana wa da manyan 'yan siyasa gabanin zaben 2027

"Magoya bayan Kwankwaso sun ragu," APC

APC ta bayyana cewa Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ba shi da yawan magoya bayan da ake zuzuta cewa ya na da su a halin yanzu.

Jam'iyyar, reshen jihar Kano ta ce jar hula ta na da daukar ido, saboda haka wannan ce ke sanya wa ana kallon tsirarun mutane kamar masu yawa.

Ahmed S Aruwan ya ce:

"Kwankwaso ya na da masu jar hula a ka, kuma in ka tara mutum 100 ka sa masu jar hula, sai a gansu har, kamar sun kai mutum 1,000.
"Ki zagaya kananan hukumomin Kano 44, duk inda dan Kwankwasiyya ya ke ai mun san shi.

Ya kara da cewa APC ta san karfin Kwankwaso, kuma ta na sane da iya yawan mutanen da ke goyon bayansa a jihar Kano.

S Aruwan ya nanata cewa za su kawo kujerar shugaban kasa a zaben 2027, kuma hakan za ta tabbata ba tare da gudunmawar Sanata Kwankwaso da mutanensa ba.

Kara karanta wannan

"Tinubu zai sha wahala": LP ta bayyana wanda za ta tsayar takarar shugaban ƙasa a 2027

APC: 'Rabiu Kwankwaso ba ya tsorata mu'

A wani labarin, kun ji cewa jam'iyyar APC ta yi martani ga tattaunawar Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso da wasu manyan 'yan siyasa a kasar nan, inda ta ce lamarin ba ya girgiza ta ko kadan.

A kwanakin baya, Jagoran Kwankwasiyya kuma tsohon dan takarar shugaban kasa da ya kawo wa APC cikas a Kano, Rabi'u Musa Kwankwaso ya gana da tsohon gwamnan APC, Rauf Aregbesola.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

iiq_pixel