APC na Yi wa Jam'iyyar Adawa Dauki Dai Dai, Dan Majalisar PDP Ya Sauya Sheka

APC na Yi wa Jam'iyyar Adawa Dauki Dai Dai, Dan Majalisar PDP Ya Sauya Sheka

  • Shugaban majalisar wakilai, Tajudeen Abbas ya sanar da cewa jam'iyyarsa ta samu karuwa bayan wani dan majalisa ya fice daga PDP
  • Dan majalisar wakilai daga jihar Kebbi, Garba Koko, ya bar PDP saboda wasu dalilai da ya ke ganin ba za su bari ya ci gaba da zama a cikinta
  • Amma shugaban marasa rinjaye, Kingsley Chinda ya ce abin da ke gudana a PDP, shi ake gani a dukkanin jam'iyyun kasar nan, har da APC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Wani dan majalisar wakilai daga jihar Kebbi, Garba Koko, ya bi sahun takwarorinsa wajen sauya sheka daga PDP zuwa APC.

Shugaban majalisar wakilai, Tajudeen Abbas, ya sanar da sauyin shekar Garba Koko cikin wata wasika da ya karanta a zaman majalisa da ya gudana a ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Arewa: El-Rufa'i ya aika gargadi ga APC da Tinubu kan zaben 2027

Ganduje
APC ta samu karuwa da dan majalisar PDP Hoto: @OfficialAPCNg
Asali: Facebook

Jaridar The Cable ta wallafa cewa Hon. Garba Koko na wakiltar mazabar tarayya ta Besse/Maiyama Yema a jihar Kebbi a zauren majalisar wakilan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin dan majalisar PDP na komawa APC

Business day ta ruwaito cewa dan majalisar ya bayyana cewa ya yanke shawarar barin PDP ne saboda rikicin cikin gida da ya ya-ki-ci, ya ki cinyewa a jam’iyyar.

Sai dai shugaban marasa rinjaye a majalisar, Kingsley Chinda, ya musanta ikirarin Garba Koko, yana cewa babu wani rikicin da ya dade yana gudana a PDP.

Ya ce:

“Dole ne a gyara wannan fahimtar don kuskure ne. Babu rikicin da ya dade a PDP.”

Jam'iyyar PDP ta yi martani ga dan majalisa

Shugaban marasa rinjaye, Kingsley Chinda, ya ce dukkan jam’iyyu a kasar nan, ciki har da APC da LP, suna da rikice-rikicen cikin gida.

Ya bukaci kakakin majalisar wakilan da ya bayyana kujerar dan majalisar da ya sauya sheka a matsayin babu kowa a cikinta.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC ta jijjiga PDP a Kaduna, dan majalisar tarayya ya sauya sheka

Ya ce hakan zai zo daidai da tanadin sashe na 68 na kundin tsarin mulkin 1999 da ke fayyace sharudan da za su iya sa dan majalisa ya rasa kujerarsa.

“Majalisar ta aiwatar da kundin tsarin mulki ta hanyar bayyana kujerar a matsayin babu kowa. Kada mu ci gaba da kafa mummunan al’ada,."

- Kingsley Chinda

Majalisa ta yi martani a kan sauyin shekar

Da yake mayar da martani, shugaban majalisar wakilan Najeriya, Tajudeen Abbas ya ce kotu ce kadai ke da ikon soke kujerar wani dan majalisa.

Sauyin shekar Garba Koko ya biyo bayan sauyin shekar Amos Magaji na Kaduna daga PDP zuwa APC da aka sanar awanni 24 da su ka gabata.

A makonnin da suka gabata, da dama daga cikin wasu ‘yan majalisa sun sauya sheka daga PDP da LP zuwa APC.

Majalisa ta damu da rashin tsaro a Borno

A wani labarin, mun ruwaito cewa Majalisar wakilai ta yi kira ga gwamnatin tarayya kan matsalar rashin tsaro da ake fama da ita a wasu yankunan jihar Borno da wasu sassan Arewa.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Gombe ta fusata, an ba da umarnin farauto makasan malamin addini

Dan majalisa mai wakiltar Askira-Uba/Hawul, Midala Balami, wanda ya gabatar da kudirin, ya bayyana yadda ƴan ta'addan Boko Haram suka kai hari kan wasu ƙauyuka a Hawul.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

iiq_pixel