PDP Ta Kara Birkicewa bayan Dakatar da Shugaban Kwamitin Amintattu, An Fadi Zunubinsa

PDP Ta Kara Birkicewa bayan Dakatar da Shugaban Kwamitin Amintattu, An Fadi Zunubinsa

  • Jam'iyyar PDP reshen jihar Abia ta ɗauki matakin ladabtarwa kan shugaban kwamitin amintattu (BoT), Sanata Adolphus Wabara
  • PDP ta dakatar da Sanata Wabara bisa zargin yi mata zagon ƙasa tare da cire shi daga muƙamin shugaban kwamitin BoT na kasa
  • Shugaban PDP a Abia, Elder Amah Abraham ya bayyana cewa an dakatar da Sanata Wabara ne bisa zargin yi wa jam'iyyar zagon ƙasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Abia - Jam’iyyar PDP reshen jihar Abia ta dakatar da shugaban kwamitin amintattu (BoT) na PDP, Sanata Adolphus Wabara.

Jam'iyyar PDP ta dakatar da Sanata Adolphus Wabara ne bisa zargin yi mata zagon ƙasa.

PDP ta dakatar da Adolphus Wabara
PDP ta dakatar da shugaban kwamitin amintattu (BoT) Hoto: @OfficialPDPNig
Asali: Twitter

An bayyana dakatarwar ne bayan wani taron kwamitin zartarwa (SEC) na PDP na jihar Abia wanda aka gudanar a birnin Umuahia, cewar rahoton jaridar Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jam’iyyar PDP ta ce wasu abubuwan da Wabara ke yi ba su dace da matsayinsa na tsohon shugaban majalisar dattawa kuma shugaban kwamitin BoT na jam’iyyar ba.

Kara karanta wannan

NNPP: "Har yanzu Kwankwaso, Abba halastattun 'yan jam'iyya ne"

Dalilan PDP na dakatar da Sanata Wabara

A cewar jam’iyyar, daga cikin dalilan da suka jawo yanke wannan hukunci shi ne Wabara ya fito fili ya bayyana cewa gwamnan jihar Abia, Dr. Alex Otti na jam’iyyar LP ya riga ya lashe zaɓe wa’adi na biyu.

Baya ga haka, jam’iyyar ta ce an ba Wabara lokaci don ya nemi afuwa bisa waɗannan laifuka, amma ya ƙi ya yi hakan, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar.

Shugaban PDP na jihar Abia, Elder Amah Abraham, ya bayyana cewa jam’iyyar za ta kafa kwamitin bincike mai mutum bakwai domin duba zarge-zargen da ake yi wa Wabara.

An cire Wabara daga shugaban BoT

Shugaban na PDP ya bayyana cewa bisa tanadin sashe 59(1) (e) da (f) na kundin tsarin mulkin jam'iyyar (wanda aka yi wa gyara a 2017), an haramtawa Wabara riƙe wani muƙami a jam'iyyar sannan an cire shi daga muƙamin shugaban kwamitin BoT.

"Duba da irin girman zagon ƙasan da Wabara ya yi wa jam'iyya, kwamitin SEC ya yi amfani da tanade-tanaden sashe na 57(1),(2),(3), 58(1)(b) & (f) da 59(1) na kundin tsarin mulkin jam’iyyar domin dakatar da shi daga duk wasu harkokin jam’iyya.”

Kara karanta wannan

'Yadda gwamnonin PDP ke shirin kafa sabuwar jam'iyya domin komawa cikinta'

"Hakazalika bisa tanade-tanaden sashe na 59(1) (e) da (f) na PDP, an haramtawa Sanata Adolphus Wabara riƙe wani muƙami a jam'iyyar da cire shi daga muƙamin shugaban kwamitin BoT na PDP."

- Elder Amah Abraham

Sanatan PDP ya koma jam'iyyar APC

A wani labarin kuma, kun ji cewa sanatan da ke wakiltar Delta ta Arewa a majalisar dattawa, Sanata Ned Nwoko ya sauya sheƙa daga jam'iyyar PDP zuwa APC.

Sanata Ned Nwoko ya koma jam'iyyar APC ne a hukumance a zauren majalisar dattawa yayin zamanta na ranar Laraba, 5 ga watan Fabrairun 2025.

Ned Nwoko dai ya samu nasarar lashe kujerar sanata ne a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar PDP a zaɓen 2023 kafin alakarsa da gwamnati tayi tsami.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng