'Komai Ya Wuce': El Rufai Ya Fadi Manyan Dalilai 3 na Tallata Tinubu a Zaben 2023

'Komai Ya Wuce': El Rufai Ya Fadi Manyan Dalilai 3 na Tallata Tinubu a Zaben 2023

  • Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, ya karyata masu zargin cewa bai goyi bayan shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2023 ba
  • Mallam Nasir El-Rufai ya ce ya yi abin da ya yi don Allah, ƙasa da jam’iyya ne ba tare da tsammanin samun komai daga kowa ba
  • Dan siyasar ya bayyana cewa abin da ke faruwa yanzu darasi ne na rayuwa, kuma lamirin masu sukarsa ba zai bar su su yi barci ba

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, ya musanta zargin cewa bai goyi bayan shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2023 ba.

El-Rufai ya ce ya riga ya wuce irin waɗannan maganganun kuma ba shi da wata boyayyar bukata kan abin da ya aikata a siyasa.

El-Rufai ya yi magana kan dalilan tallata Tinubu a zaben 2023
El-Rufai ya yi martani game da masu cewa bai tallata Tinubu ba a 2023. Hoto: @elrufai
Asali: Facebook

Ana zargin El-Rufai bai goyi bayan Tinubu ba

Kara karanta wannan

Dan El Rufai ya fadi matsayarsa kan bincikar mahaifinsa ya ba da shawara

Tinubu ya lashe zaɓen shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar APC, inda ya doke Atiku Abubakar na PDP da Peter Obi na Labour Party, inji rahoton Arise News.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

El-Rufai, wanda ya taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da Tinubu ya samu tikitin APC, ya ce ra’ayinsa kan tafiyar da mulki ba zai canza ba.

Wani ma'abocin X (Twitter) mai suna Yusuf Tukur ya yi ikirarin cewa Tinubu da magoya bayansa sun nemi goyon bayan El-Rufai kafin zaɓen, amma daga baya suka ce bai goyi bayansu ba.

Dalilin El-Rufai na tallata Tinubu a 2023

El-Rufai ya mayar da martani ta shafinsa na X yana cewa ya yi abin da ya yi don Allah, ƙasa da jam’iyya, ba don wata riba ba.

"Mun yi abin da muka yi don Allah, ƙasa da jam’iyya, ba tare da tsammanin samun komai daga wajen kowa ba," inji El-Rufai.

Kara karanta wannan

Dan tsohon gwamna, Bello ya fadi matsayarsa kan rigimar El Rufai da Uba Sani da ake yi

Ya kara da cewa abin da ke faruwa yanzu wani darasi ne na rayuwa, yana mai cewa "muna ci gaba da rayuwarmu, amma lamirin su ba zai bar su su yi barci lami lafiya ba."

El-Rufai ya ce komai ya wuce, kuma tuni ya manta da ire-iren wadannan maganganun, yana mai godewa Allah kan duk abin da ya faru.

'El-Rufai bai da tasiri yanzu a siyasa' - Bwala

A wani labarin, mun ruwaito cewa mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai, Daniel Bwala, ya soki tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai.

Daniel Bwala ya yi ikirarin cewa yanzu El-Rufai ba shi da sauran tasiri a siyasa, har ma ba zai iya lashe kujerar sanata idan da zai fito takara ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

iiq_pixel