Dan Takarar Shugaban Kasa Ya Ragargaji Tinubu kan Yawan Karbar Haraji

Dan Takarar Shugaban Kasa Ya Ragargaji Tinubu kan Yawan Karbar Haraji

  • Tsohon dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar SDP, Adewole Adebayo, ya bukaci gwamnatin Tinubu da ta fi maida hankali kan bunkasa tattali
  • Adewole Adebayo ya ce tattalin arziki na bukatar saukaka rayuwar al’umma domin samar da ci gaba mai dorewa ba wai kawai tattara haraji ba
  • Ya soki yadda gwamnati ke mayar da hankali kan karbar haraji fiye da inganta ayyukan noma, fasaha da sufuri da 'yan kasa za su ci moriya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Tsohon dan takarar shugaban kasa a SDP, Adewole Adebayo, ya bukaci gwamnatin tarayya da ta daina maida hankali kan karbar haraji daga jama’a.

Adewole Adebayo ya kuma yi kira a mayar da hankali kan habaka tattalin arziki ta hanyar bunkasa masana’antu da inganta rayuwar al’umma.

Kara karanta wannan

Nnamdi Kanu ya tayar da kura a kotu, ya nuna tirjiya a gaban alkali

Adewole Adebayo
Dan takarar SDP ya bukaci Tinubu ya sauya salo kan karbar haraji. Hoto: Bayo Onanuga|Adewole Adebayo
Asali: Facebook

A cewar rahoton jaridar Daily Trust, Adebayo ya yi wannan bayani ne a Abuja yayin da yake zantawa da manema labarai, inda ya soki salon tafiyar da tattalin arzikin kasar nan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Adebayo ya bayyana cewa karbar haraji ba shi ne tushen ci gaban kasa ba, inda ya ce idan gwamnati ta samar da yanayi mai kyau ga ‘yan kasa, hakan zai haifar bunkasan tattali.

Adebayo ya nemi a inganta rayuwar jama'a

Adewole Adebayo ya ce kamata ya yi gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta fahimci cewa tattalin arziki ba wai kawai karbar kudi daga jama’a ba ne.

Ya ce ya kamata Bola Tinubu ya gano cewa akwai bukatar samar da abubuwan more rayuwa da za su tallafawa cigaban kasa.

Adewole Adebayo ya ce:

“Idan ana son ci gaba mai dorewa, wajibi ne gwamnati ta ba da fifiko kan saukaka rayuwar jama’a.

Kara karanta wannan

Tsohon gwamnan APC ya tona sirrin 'sabanin' da ke tsakanin 'yan siyasa

"Idan mutane na da ruwan sha mai tsafta, hakan yana rage yawan cututtuka. Idan akwai isasshen abinci, hakan yana karfafa lafiyar mutane.”

Adebayo ya yi magana kan tattara haraji

Adewole Adebayo ya soki yadda gwamnati ke fifita karbar haraji a kan bunkasa tattalin arziki inda ya ce:

“A yanzu gwamnatin tarayya ta mayar da hankali kan karbar haraji, alhali kamata ya yi ta fi maida hankali kan samar da damammaki ga ‘yan kasa.
“A tattalin arzikin duniya, akwai bambanci tsakanin abin da ya dace da kamfani da abin da ya dace da al’umma.
Idan gwamnati na kallon kanta a matsayin kamfani da ke bukatar tara kudi kawai, hakan kuskure ne."

Yawan haduran mota a Najeriya

Adebayo ya bayyana yadda rashin kyawun hanyoyi da tsadar sufuri ke hana ci gaban tattalin arziki.

Ya ce dole ne gwamnati ta samar da wutar lantarki mai sauki, gidaje masu araha, da hanyoyi masu kyau.

Kara karanta wannan

"Jihohi za su fara gasa," Gwamnati ta ce kudirin haraji zai farfado da tattalin arziki

Adebayo ya ce:

“Idan ka zagaya Najeriya, za ka ga tarin manyan motocin dakon kaya ta ko ina.
Tsadar man dizil yana sanya masu motocin dakon kaya yin asara, don haka sai su yi lodi fiye da kima. Wannan kuwa yana haddasa hadura, jinkiri da asarar kaya.”

Saraki ya ba Tinubu shawari kan haraji

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata Abubakar Bukola Saraki ya bukaci gwamnati a kan karin harajin hukumar kwastam.

Bukola Saraki ya ce karin haraji na 4% da hukumar kwastam ta yi zai kara jefa Najeriya a cikin masifar tsadar kayayyaki da aka dade ana fama da shi a kasar nan.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

iiq_pixel