Kwankwaso Ya Gana da Tsohon Gwamnan APC, an Yi Hasashen Shirin Tumbuke Tinubu
- Tsohon gwamnan Osun, Rauf Aregbesola da Rabiu Kwankwaso sun gana a Legas da ake zargin bai rasa nasaba na zaben 2027
- Ganawar ta kasance mai tsawo inda jiga-jigan siyasar suka tattauna batutuwa masu muhimmanci game da makomar siyasa a Najeriya
- Ana sa ran karin bayani daga bangarorin da suka halarci wannan ganawa, yayin da ake ci gaba da shirye-shiryen babban zaben kasa
- Wannan na zuwa ne yayin da wasu ke hasashen hadakar jam'iyyun adawa da matsalar Aregbesola da APC
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Ikeja, Lagos - Tsohon gwamnan Osun, Rauf Aregbesola ya yi muhimmiyar ganawa da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
Tsohon ministan harkokin cikin gida da Rabiu Kwankwaso sun gana a Lagos domin “tsara dabaru” kafin zaben 2027.

Source: Twitter
APC ta kori Aregbesola daga jam'iyyar
TheCable ta tabbatar da cewa wasu majiyoyi sun tabbatar da cewa an yi ganawar saboda zaben 2027 mai zuwa.
Wannan na zuwa ne bayan jam'iyyar APC ta kori tsohon gwamnan na jihar Osun bisa zargin cin dunduniyarta da kuma wasu zarge-zarge da ake yi masa.
Kwamitin gudanarwa na APC na Osun ya ce an ɗauki matakin korar Aregbesola ne bayan samun rahoto kan binciken da aka yi a kansa.
2027: Kwankwaso ya gana da Aregbesola a Lagos
An gudanar da taron a yau Asabar 8 ga watan Janairun 2025 wanda aka shafe fiye da awa daya ana ganawar a Lagos, cewar The Guardian.
Duk da yake ba a fitar da cikakkun bayanai ga manema labarai ba, majiyoyi sun ce hakan na da alaka da shirin shiga jam’iyyar NNPP da Aregbesola da magoya bayansa ke yi.
A kwanakin baya, an yi ta rade-radin cewa Aregbesola da magoya bayansa na iya komawa NNPP kafin zaɓen gwamnan Osun na badi.
“Aregbesola da Kwankwaso sun gama wani dogon taro a Lagos inda suka tsara dabarun zaben 2027."
- Cewar wata majiya
Tsohon kwamishinan Ganduje ya koma layin Kwankwaso
Kun ji cewa tsohon kwamishinan shari'a a gwamnatin Abdullahi Ganduje, Barista Haruna Isah Falali, ya sauya sheƙa zuwa jam'iyyar NNPP.
Jagoran jam'iyyar NNPP na ƙasa, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, ya karɓi Haruna Isa Falali da kansa a gidansa da ke Abuja.
Yan Kwankwasiyya sun nuna farin ciki da shigowar Falali jam'iyyarsu, suna addu'ar hakan ya haifar da nasara a tafiyarsu.
Asali: Legit.ng

