Shugaban NNPP Ya Tabbatar da Korar Kwankwaso da Buba Galadima a Jam'iyya

Shugaban NNPP Ya Tabbatar da Korar Kwankwaso da Buba Galadima a Jam'iyya

  • Shugaban tsagin jam’iyyar NNPP na kasa, Agbo Major, ya jaddada da cewa sun kori Sanata Rabiu Kwankwaso da bangarensa a tafiyarsu a Najeriya
  • Hakan na zuwa ne bayan bangaren Kwankwaso ya ce taron da Agbo ya jagoranta a Legas ba bisa ka’ida ba ne, yana mai cewa Dr Ajuji Ahmed ne shugaban NNPP
  • Sai dai Agbo Major ya ce an gudanar da taron ne bisa hukuncin kotu, kuma an tabbatar da korar Kwankwaso da mayar da tsohon tambarin jam’iyyar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Shugaban jam’iyyar NNPP na kasa, Agbo Major, ya jaddada korar tsohon dan takarar shugaban kasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, da bangarensa daga jam’iyyar.

Agbo Major ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Abuja, inda ya ce taron da aka gudanar a Legas a ranar Talata ya halatta bisa hukuncin kotu.

Kara karanta wannan

'Ka taka masa birki': An kai karar El Rufai gaban Nuhu Ribadu, an hango hatsarin kalamansa

Kwankwaso
Tsagin NNPP ya jaddada korar Kwankwaso. Hoto: Saifullahi Hassan
Asali: Facebook

Punch ta wallafa cewa bangaren Kwankwaso ya musanta hakan, yana mai cewa taron bai yi daidai da doka ba, kuma Dr Ajuji Ahmed ne kadai shugaban jam’iyyar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Taron Legas da sabanin bangarorin NNPP

A ranar Talata ne jam’iyyar NNPP ta gudanar da taronta na kasa a jihar Legas, inda aka zabi Agbo Major a matsayin sabon shugaban jam’iyyar.

Sai dai bangaren Kwankwaso ya bayyana cewa taron ba shi da inganci, yana mai cewa har yanzu Dr Ajuji Ahmed ne sahihin shugaban jam’iyyar.

Mai magana da yawun bangaren, Ladipo Johnson, ya bayyana cewa bangaren Major "kungiyar ‘yan tawaye" ne, kuma ba su da wata madafa ta doka a jam’iyyar.

Amma a nasa bangaren, Agbo Major ya ce taron ya kasance bisa ka’ida, yana mai cewa kotu ta ba su damar gudanar da shi.

Shawarwarin kotu da matakin jam'iyyar NNPP

Kara karanta wannan

Siyasar Kano: Kwankwaso ya karbi kwamishinan Ganduje a jam'iyyar NNPP

Agbo Major ya bayyana cewa hukuncin babbar kotun Abia da aka yanke a ranar 1 ga watan Nuwamba 2024 ya umurci hukumar INEC da ta mika jam’iyyar ga kwamitin amintattu.

A cewar Agbo, kwamitin amintattun yana karkashin jagorancin Dr Boniface Okechukwu Aniebonam.

Ya ce kotun ta umarci kwamitin amintattu da su dawo da dukkan tsare-tsaren jam’iyyar kamar yadda kundin tsarin mulkinta na 2022 ya tanada.

Bisa ga hakan, Agbo Major ya ce jam’iyyar ta bi tsarin doka, inda aka fara gudanar da zabe daga matakin mazabu a ranar 13 ga Janairu 2024.

Korar Kwankwaso da sauya tambarin NNPP

Daga cikin muhimman abubuwan da aka cimma a taron, Agbo Major ya ce an tabbatar da korar Kwankwaso, Buba Galadima, da dukkan bangaren Kwankwasiyya daga jam’iyyar.

Ya ce an kuma yi bitar kudinjam’iyyar, tare da yanke hukuncin mayar da tsohon tambarin NNPP wanda ke dauke da 'kwandon 'ya'yan itatuwa a cikin taswirar Najeriya'.

Kara karanta wannan

Kotu za ta yanke hukunci kan shari'ar mabarata da Minista bayan korafin Abba Hikima

A cewarsa, kwamitin amintattu ya kammala dukkan ayyukan da kotu ta dora musu a ranar 4 ga Fabrairu 2025, kuma an mika sakamakon taron ga hukumar INEC.

A karshe, Agbo Major ya shawarci sauran magoya bayan Kwankwasiyya da su fice daga jam’iyyar cikin lumana, kamar yadda shugabanninsu suka yi.

Kwamishinan Ganduje ya koma NNPP

A wani rahoton, kun ji cewa Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya karbi tsohon kwamishinan Ganduje zuwa jam'iyyar NNPP.

Rahotanni sun nuna cewa Kwankwaso ya karbi Barista Haruna Isa Falali ne yayin da ya sauya sheka a gidansa da ke birnin tarayya Abuja.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng