Hadimin Tinubu Ya Yi Wa El Rufai Wankin Babban Bargo, Ya Fadi Wani Sirrinsa
- Mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai, Daniel Bwala, ya sake caccakar Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai
- Daniel Bwala ya bayyana cewa tsohon gwamnan na jihar Kaduna bai da wani tasiri a yanzu, domin ko kujerar sanata ba zai iya lashewa ba
- Hadimin na Tinubu ya bayyana cewa shugaban ƙasan bai damu ba ko kaɗan kan kalaman da El-Rufai yake yi a cikin ƴan kwanakin nan
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Mai ba Shugaba Bola Tinubu shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Daniel Bwala, ya sake taso Nasir El-Rufai, a gaba.
Daniel Bwala ya bayyana cewa tsohon gwamnan na jihar Kaduna, ba shi da ƙarfin da zai iya kawar da Shugaba Bola Tinubu daga kan mulki.

Asali: Facebook
Daniel Bwala ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da tashar TVC News a a ranar Alhamis, 6 ga watan Fabrairun 2027.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tinubu bai damu da kalaman El-Rufai ba
Ya ƙara da cewa Tinubu ba ya rasa barci saboda sukar da El-Rufai ke yi wa gwamnatinsa ba tare da ƙaƙƙautawa ba.
A cikin ƴan kwanakin dai, El-Rufai ya kasance yana caccakar wasu mambobin gwamnatin Tinubu.
Da aka tambaye shi ko fadar shugaban ƙasa ta damu kan kalaman El-Rufai da shirin ƴan adawa na haɗewa, hadimin shugaban ƙasan ya ce Tinubu bai damu da abin da ƴan adawan ke ƙullawa ba.
“Wane ne ke jin tsoro? Ƴan adawa ba su da alƙibla. Babu wata jam’iyyar siyasa da ta shirya a Najeriya sai APC. Kusan dukkan jam’iyyun adawa lalube suke yi kan abin da za su yi."
“Ba na tanka musu saboda na fahimci cewa shugaban ƙasa mai son sulhu ne. A cikin watanni 18 da ya yi a ofis, bai taɓa mayar da martani ga kowa ba. Bai taɓa faɗa da wani ba."
- Daniel Bwala
Hadimin Tinubu ya caccaki El-Rufai
Mai magana da yawun shugaban ƙasar ya ce ya fahimci halin da El-Rufai ya tsinci kansa a ciki, inda ya ce tsohon gwamnan ba zai iya cimma burinsa ba idan ya koma ɓangaren ƴan adawa.
“Kamar yadda El-Rufai ya fada, har yanzu yana cikin APC. Dole ne a ɗauke shi a matsayin ɗan uwa. Na san irin salon siyasar da yake yi. Na san yana cikin rudani wajen nemo mafita."
“Idan ka bar jam’iyyar da ke mulki, wacce kake da tasiri a cikinta, kuma ka yi tunanin za ka iya cimma wata manufa, dole ne ka samu wuri mai ƙarfi da zai taimaka maka."
“Ba shi da karfin da zai sa shugaban ƙasa ya damu. Babu wata jam’iyyar adawa, ko da sun haɗe waje ɗaya, da za ta iya sa shugaban ƙasa ya damu.
“Bari na faɗa maka wani abu dangane da babban yayana El-Rufai, wanda hakan zai nuna ko ya kamata mu damu da shi."
“Akwai wata ɗabi’a ta siyasa da ke tare da El-Rufai. El-Rufai yana buƙatar ya raɓu da wani kafin ya yi suna. A karan kansa, ba zai iya lashe zaɓen sanata ba."
“Ya lashe zaɓen gwamna ne saboda tasirin Buhari, kuma ya sake lashewa ne saboda tasirin Buhari. Idan aka bar shi yanzu ya tsaya takarar sanata a Kaduna, ba zai ci ba."
- Daniel Bwala
El-Rufai ya ƙaryata Nuhu Ribadu
A wani labarin kuma, kun ji cewa Nasir El-Rufai ya shiga cikin taƙaddamar da ke tsakanin Nuhu Ribadu da Hajiya Naja'atu Muhammad.
Tsohon gwamnan na Kaduna ya ƙaryata Nuhu Ribadu bayan ya yi iƙirarin cewa bai taɓa kiran Bola Tinubu a matsayin maras gaskiya ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng