"Ka Yi Zamanka a PDP," Sanata Ya Gargaɗi Gwamnan da Ake Raɗe Raɗin Zai Koma APC

"Ka Yi Zamanka a PDP," Sanata Ya Gargaɗi Gwamnan da Ake Raɗe Raɗin Zai Koma APC

  • Sanatan Delta ta Arewa, Ned Nwoko, wanda ya sauya sheka zuwa APC, ya fara cika baki kan waɗanda ya dace su shigo jam'iyya mai ci
  • Da yake jawabi a hedkwatar APC da ke Abuja, Sanata Nwoko ya ce jam'iyyar ba ta bukatar Gwamna Sheriff Oborevwori ya dawo cikinta
  • Ya ce gara gwamnan ya ci gaba da zama a PDP, inda ya bayyana cewa an nuna masa wariya a siyasar jihar Delta shiyasa ya sauya sheka

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Sanata mai wakiltar mazaɓar Delta ta Arewa, Ned Nwoko, ya bayyana cewa jam'iyyar APC ba ta buƙatar gwamnan jiharsa, Sheriff Oborevwori, ya shigo cikinta.

A jiya Laraba, 5 ga watan Fabrairu, 2025 ne Sanata Ned Nwoko ya tabbatar da sauya sheƙarsa daga PDP zuwa APC a wasiƙar da ya miƙawa Majalisar Dattawa.

Kara karanta wannan

Ganduje ya fadi jihar da suka shirya kwatowa, ya lissafa nasarorin Tinubu

Sanata Nwoko da gwamnan Delta.
Sanata Nwoko ya caccaki gwamnan Delta, ya ce APC ba ta bukatar ya koma cikinta Hoto: Ned Nwoko, Sheriff Oborevwori
Source: Facebook

A rahoton Vanguard, Ned Nwoko ya ce a yanzu yana jinsa a matsayin ɗan gida kuma APC ba ta buƙatar gwamnan Delta ya shigo cikinta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Nwoko ya yi wannan furuci ne yayin da ya kai ziyara hedkwatar jam'iyyar APC ta ƙasa da ke birnin tarayya Abuja, inda ya haɗu da ƴan kwamitin gudanarwa.

A lokacin ziyarar, kwamitin gudanarwa na Ƙasa (NWC) ƙarƙashin jagorancin Dr. Abdullahi Ganduje ya karɓe shi a hukumance zuwa cikin jam’iyyar APC, rahoton Punch.

APC ba ta bukatar gwamnan jihar Delta

Da yake jawabi, Sanata Nwoko ya tabbatar da cewa akwai jita-jita da ke nuna cewa gwamnan Delta na shirin dawowa APC, amma ya ce ba a buƙatarsa a cikin jam’iyya mai mulki.

A cewarsa:

“Dalilin da ya sa na baro PDP shi ne domin in samu isasshen lokaci na yin wasu ayyuka ta hannun gwamnatin tarayya. Na gaji da zama a siyasar jihar Delta yadda ka san ina tsagin adawa.

Kara karanta wannan

"Waye sakataren PDP?" Barau Jibrin ya zaƙalƙale da hatsaniya ta ɓarke a Majalisar Dattawa

"Idan na faɗa ma su ga abin da ya kamata su yi, sai su yi banza da ni, shiyasa na ga ya kamata na tattara na canza wuri."

Sanata Nwoko ya caccaki Gwamna Oborevwori

Da aka tambaye shi ko zai yi maraba gwamna Oborevwori idan ya sauya sheƙa zuwa APC kamar yadda ake yayatawa, Nwoko ya kada baki ya ce:

"A’a, ba zan yi maraba da shi ba. Ta yaya? Me ya sa? Na sha gaya muku cewa bai cancanci zama gwamnan ba a halin da muke ciki. Ya gaza yin abin da aka yi tsammani tun da ya hau madafun iko."
“Da akwai wasu ayyuka da na faɗa masa cewa ana buƙatar su don amfanin jama’a, amma ya ƙi aiwatar da su," in ji Nwoko.

Menene dalilin sauya shekar Sanata Nwoko?

A wani labarin, kun ji cewa hadimin gwamnan Delta ya soki Sanata Ned Nwoko da ya sauya sheka daga PDP zuwa APC.

Ya ce ba rikicin cikin gida ya kori sanatan daga jam'iyyar PDP sai dai tsoron rasa rikitin takara a babban zaben 2027 mai zuwa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262