Ganduje Ya Fadi Jihar da Suka Shirya Kwatowa, Ya Lissafa Nasarorin Tinubu
- Shugaban jam'iyyar APC, Abdullahi Ganduje ya karbi Sanata Ned Nwoko da ya sauya sheƙa daga PDP zuwa APC saboda rikicin shugabanci
- Abdullahi Ganduje ya ce jam’iyyar APC za ta ci gaba da ƙarfafa kanta a Delta da ma sauran jihohi Najeriya da ke karkashin 'yan adawa
- Ganduje ya bayyana cewa APC za ta karɓi mulkin jihar Delta a zaɓen gwamna mai zuwa kasancewar ta samu karin Sanatoci a jihar
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Dr. Abdullahi Ganduje, ya karɓi Sanata Ned Nwoko a hukumance cikin jam’iyyar bayan sauya sheƙarsa daga PDP.
Sanatan da ke wakiltar Delta ta Arewa ya bayyana cewa ya bar jam’iyyarsa ta PDP ne saboda rikicin shugabanci da ke ci gaba da ƙara dagula tafiyar ta.

Kara karanta wannan
"Waye sakataren PDP?" Barau Jibrin ya zaƙalƙale da hatsaniya ta ɓarke a Majalisar Dattawa

Source: Twitter
Punch ta rahoto cewa Nwoko ya ce gwamnan Delta, Sheriff Oborevwori, da tsohon gwamna Ifeanyi Okowa, ba su ba shi cikakken damar da zai yi aiki yadda ya kamata a matsayin Sanata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yayin tarbar Nwoko, Ganduje ya bayyana cewa jam’iyyar APC ta kara karfi a jihar Delta, kuma za ta lashe zaben gwamna mai zuwa.
Dalilan sauya sheƙar Sanata Ned Nwoko
Sanata Nwoko ya bayyana cewa ya yanke shawarar barin PDP ne bayan yin dogon nazari da tuntubar jama’ar da yake wakilta a yankin Delta ta Arewa.
"PDP jam’iyya ce da ta kasance ginshiƙi ga dimokuraɗiyya da ci gaban ƙasa, amma rikicin shugabanci da rashin tsari sun mamaye ta.
"Saboda haka, na ga dacewar barinta domin komawa jam’iyya mai tsari da nagarta,"
- Sanata Nwoko
Sanatan ya bayyana cewa matsalolin da suka dabaibaye PDP sun hana shi damar aiki yadda ya kamata, don haka ya ga cewa sauya sheƙa zuwa APC shi ne mafi alheri.
Ganduje ya ce APC za ta kwace jihar Delta
Shugaban APC na ƙasa, Dr. Abdullahi Ganduje, ya ce jam’iyyar na cikin shirin lashe jihar Delta a babban zaɓen gwamna mai zuwa.
"Muna farin cikin tarbar Sanata Nwoko cikin jam’iyyar APC. Ba shakka, shugaban ƙasa Bola Tinubu jagora ne mai hangen nesa.
"Yana hawa mulki ya ɗauki matakan da suka dace duk da cewa za su jawo wahalar dan kankanin lokaci,"
- Abdullahi Ganduje
Premium Times ta wallafa cewa Ganduje ya ƙara da cewa manufofin Tinubu sun fara haifar da sakamako mai kyau, inda ya ce:
"Mun fara ganin ci gaba daga irin waɗannan sauye-sauyen. Fetur da ake hakowa ya ƙaru, matatun mai sun fara aiki, kuma tsaro yana ingantuwa.
"Haka nan, APC a jihar Delta za ta tabbatar da ingantaccen tsari na dimokuraɗiyya."
Ganduje ya bayyana cewa kasancewar APC tana da dukkan sanatocin jihar Delta zai taimaka wajen kwace ikon jihar a zabe mai zuwa.

Kara karanta wannan
"Gwamna da abokin takarar Atiku na roƙon a bari su shigo APC," Sanata ya ce babu wurinsu
"A baya muna da sanatoci biyu daga jihar Delta, amma yanzu muna da guda uku. Mun kuduri aniyar karɓar mulkin jihar Delta gaba ɗaya,"
- Abdullahi Ganduje
Siyasar Kaduna ta dauki sabon salo
A wani rahoton, ku ji cewa yanayin siyasar jihar Kaduna ya fara daukar sabon salo yayin da Nasir El-Rufa'i ya yi martani ga gwamna Uba Sani.
Tsohon gwamnan ya yi magana ne bayan gwamnan jihar na yanzu, Uba Sani ya bayyana cewa babu wani sabani a tsakaninsu a halin yanzu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng
