2027: Masari Ya Taso Masu Son Kawar da Tinubu a Gaba, Ya Fadi Makomarsu

2027: Masari Ya Taso Masu Son Kawar da Tinubu a Gaba, Ya Fadi Makomarsu

  • Tsohon gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari ya bi sahun masu yin magana kan shirin wasu ƴan siyasa na kawar da Bola Tinubu a 2027
  • Aminu Bello Masari ya bayyana ƴan siyasan a matsayin waɗanda suka rasa tudun dafawa a jam'iyyar APC
  • Tsohon gwamnan na jihar Katsina ya bayyana cewa babu wata jam'iyya da za ta iya maye gurbin jam'iyyar APC a Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Katsina - Tsohon gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya yi magana kan shirin wasu ƴan siyasa na samar da sabuwar jam'iyya.

Aminu Bello Masari ya bayyana cewa babu wata jam’iyya da za ta iya maye gurbin APC a Najeriya.

Masari ya yi magana kan shirin 'yan siyasa
Masari ya ce ba zai bar APC ba Hoto: @GovernorMasari
Asali: Twitter

Masari ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi a garin Kafur, ƙaramar hukumar Kafur ta jhar Katsina, yayin ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen ciyamomi da za a gudanar a ranar 15 ga watan Fabrairu, cewar rahoton jaridar TheCable.

Kara karanta wannan

2027: Shugaban SDP ya gano abin da zai hana Tinubu sake samun nasara

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me Masari ya ce kan shirin kawar da Tinubu?

Tsohon gwamnan ya yi watsi da batun cewa wasu ƴan siyasa na ƙoƙarin haɗa kai domin kawar da APC daga mulki, yana mai cewa hakan ba komai ba ne illa haɗewar waɗanda suka rasa tagomashi a cikin jam’iyyar.

"Labaran da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa wasu ƴan siyasa na ƙoƙarin haɗewa don kafa sabuwar jam’iyya ba komai ba ne illa taron waɗanda suka rasa muƙamai ko tagomashin siyasa a APC."
“Yunƙurinsu na kafa wata ƙungiya ba zai karkatar da hankalin APC daga aiwatar da shirye-shiryen da za su rage raɗaɗin talakawa ba.”

- Aminu Bello Masari

Masari ba zai bar APC ba

Masari ya ce a matsayinsa na ɗaya daga cikin waɗanda suka kafa APC, zai ci gaba da kasancewa mai biyayya ga aƙidun jam’iyyar.

"Ina APC a yau, gobe, da har abada, domin ba na cikin jam’iyyar don neman wani muƙami."

Kara karanta wannan

Ana hasashen hadaka, jam'iyyar Kwankwaso ta yi rashi, shugaban NNPP ya koma APC

- Aminu Bello Masari

Wasu ƴan APC sun caccaki jam'iyyar

A kwanakin baya, tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi, da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, sun jawo cece-kuce bayan sukar jam’iyyar APC a wani taro da aka shirya kan ƙarfafa dimokuradiyya a Najeriya.

El-Rufai ya ce jam’iyyar APC mai mulki ta yi watsi da ƙa’idojin da aka kafa ta a kai, kuma yanzu tana goyon bayan jagoranci maras inganci.

A nasa ɓangaren, Amaechi ya ce shugaba Bola Tinubu da sauran ƴan siyasa ba za su mika mulki ga matasa ba sai an kai ruwa rana.

Tinubu ya yi fatali da shirin ƴan adawa

A wani labarin kuma, kun ji cewa fadar shugaban ƙasa ta yi fatali da shirin wasu ƴan jam'iyyar APC da na jam'iyyun adawa, kan haɗewa domin kawar da shugaba Bola Tinubu.

Fadar shugaban ƙasan ta bayyana cewa shugaba Bola Tinubu bai damu da duk wani shiri da suke ƙullawa ba, domin yanzu ba ta su yake yi ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng