Rikicin PDP: APC Ta Mika Muhimmiyar Bukata ga 'Yan Najeriya

Rikicin PDP: APC Ta Mika Muhimmiyar Bukata ga 'Yan Najeriya

  • Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta wanke kanta kan rikicin siyasa da ya addabi abokiyar hamayyarta ta PDP
  • APC ta ce ba ruwanta da hannu a rikicin na PDP, inda ta nuna cewa jam'iyyar ta kamo hanyar da za a shafe tarihinta
  • Jam'iyyar APC ta buƙaci ƴan Najeriya da ka da su sake bari PDP ta dawo kan madafun ikon ƙasar nan duba da yadda take tafiyar da al'amuranta a yanzu

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Jam’iyyar APC mai mulki ta yi magana kan rikicin shugabanci da ya dabaibaye abokiyar hamayyarta ta PDP.

APC ta bayyana PDP a matsayin jam'iyyar siyasar da ke tafiya sannu a hankali zuwa ga ɓacewa sakamakon rikicin shugabanci da ya addabe ta.

APC ta roki 'yan Najeriya kan PDP
APC ta bukaci 'yan Najeriya ka da su bari PDP ta dawo kan mulki Hoto: @OfficialAPCNg, @OfficialPDPNig
Asali: Facebook

Daraktan yaɗa labarai na APC na ƙasa, Bala Ibrahim, ne ya bayyana hakan a wata hira da ya yi da jaridar The Punch.

Kara karanta wannan

PDP ta kara hargitsewa bayan an yi harbe harbe a hedkwatar jam'iyyar, an samu bayanai

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wace buƙata APC ta nema a wajen ƴan Najeriya?

APC ta buƙaci ƴan Najeriya da su tabbatar da cewa PDP ba ta sake dawowa kan mulki ba, duba da ɓarnar da ake zargin ta bari bayan mulkin shekaru 16.

"Najeriya har yanzu tana fama da ɓarnar da PDP ta yi a cikin shekaru 16 na mulkinta. Wannan jam’iyya ta ƙare. Waɗannan ne mutanen da wasu ke tunanin za su sake mulkar wannan ƙasa?"
"Ku yarda da ni, yanzu aka fara wasan. Mu a APC muna jin daɗin wannan wasan kwaikwayon."
"Jam’iyyar PDP ba ta iya tafiyar da komai ba, har da kanta. Abin da ke faruwa ya nuna cewa Allah ne ya ceci ƴan Najeriya ta hanyar kawar da su daga mulki."
"Idan aka zurfafa bincike cikin matsalolin jam’iyyar, za a ga cewa akwai ƙarin abubuwan da za su faru. Ya kamata su zo su koyi yadda ake siyasa a cibiyar APC da Dakta Abdullahi Ganduje, ya kafa. Za a koya musu siyasa ba tare da gaba ko ƙiyayya ba."

Kara karanta wannan

'Talauci ne': Ministan Buhari ya fadi dalilin shiga siyasa, ya bugi kirji kan kafa APC

- Bala Ibrahim

Me APC ta ce kan rikicin PDP?

Da aka tunatar da shi cewa wasu na zargin APC da hannu a rikicin PDP da na sauran jam’iyyun adawa, Ibrahim Bala sai ya kada baki ya ce:

“Ta yaya APC ke da alhakin rikicin da ke faruwa a Wadata Plaza (hedikwatar PDP da ke Abuja)? Bama kusa da su ma."
"To, ta yaya za su ɗora mana laifin matsalolinsu? Me alaƙar APC da samun sakatarori biyu ko shugabanni biyu ko duk wani abin da suke da shi?
"Ba su san yadda ake tafiyar da komai ba, kuma ba za su iya ba. Wane ne daga cikin masu boren da ke riƙe da katin APC? Wane ne daga cikin masu haddasa rikicin da ke cewa yana biyayya ga APC? Babu ko ɗaya. Wannan matsala ce da ke tsakaninsu."

Gwamnonin PDP sun sha alwashi

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnonin jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya sun sha alwashi kan zaɓen shekarar 2027.

Kara karanta wannan

Tsohon ɗan Majalisa ya danƙara wa Atiku baƙaken kalamai bayan abin da ya faru a taron BoT

Gwamnonin na PDP a yayin wani taro da suka gudanar sun lashi takobin ƙwace mulki a hannun jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng