'Sun Watse Mana': Atiku Ya Fadi Abin da yan Najeriya suka yi musu yayin Kamfen Siyasa
- Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya bayyana yadda tarukan siyasa ke faruwa a Najeriya
- Atiku ya koka kan yadda magoya baya ke halartar gangamin jam'iyya don biyan bukata, ba wai kishin jam’iyya ba
- Atiku ya tuna wani taro da suka yi a Ribas, jama’a suka fice daga filin taro saboda an biya su na tsawon sa’o’i biyu ne kawai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Tsohon dan takarar shugaban kasa a PDP, Atiku Abubakar, ya yi magana kan yadda yan Najeriya ke yaudara a siyasa.
Atiku Abubakar ya bayyana yadda yan Najeriya suka watsa musu kasa a ido yayin taron siyasa a jihar Rivers da ke Kudancin Najeriya.

Asali: Getty Images
Amaechi ya koka kan yaudararsu 'yan siyasa
Atiku ya fadi haka ne a cikin wani faifan bidiyo da Punch ta wallafa yayin taron siyasa a Abuja.

Kara karanta wannan
'Talauci ne': Ministan Buhari ya fadi dalilin shiga siyasa, ya bugi kirji kan kafa APC
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsohon mataimakin shugaban kasa ya yi martani ne ga kalaman Rotimi Amaechi kan halayen yan Najeriya.
Taron, wanda Cibiyar Jagoranci da Dabaru ta Afrika ta shirya, ya mayar da hankali ne kan karfafa dimukuradiyya a Najeriya.
Amaechi ya yi magana kan yadda ake amfani da kudi wajen tara jama’a a wasu tarukan siyasa.
Ya ba da labarin wani gangami na APC a 'Eagle Square', Abuja, inda wasu mata da aka dauka suka zo da rigunan Jonathan wanda ke neman wa’adi na biyu a matsayin shugaban kasa.
“Mun yanke shawarar yin gangami, mun hadu a Eagle Square, mun fitar da kudi domin a tara jama’a.
“Na iso wurin kafin wasu, na ga taron mata. Sannu da zuwa! Sai na lura suna sanye da rigunan ‘Jonathan for President’.”
- Rotimi Amaechi
Atiku ya fadi yadda aka barin taronsu
Yayin da yake martani kan maganar Amaechi, Atiku ya amince da batun tsohon gwamnan ta hanyar ba da wani labari kan yadda ake tara jama’a a gangamin siyasa.

Kara karanta wannan
Ministan Buhari ya tona asirin yadda suka dauki hayan mata domin kifar da Jonathan
“Ina so in fada wani abu... kamar yadda aka yi a Rivers.
“Lokacin da Odili ke gwamna a Rivers, mun je wani gangami. Filin taro ya cika makil da jama’a.
“Amma kafin mu gama jawabi, kowa ya watse, Sai muka tambaya me ya faru, aka ce an biya su na sa’o’i biyu ne kawai."
- Atiku Abubakar
Atiku ya yi kaca-kaca da Tinubu
Kun ji cewa tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya soki gwamnatin Bola Tinubu kan kama Omoyele Sowore da Usman Yusuf.
Atiku Abubakar ya ce ana amfani da kama ‘yan adawa domin razana su da kuma hana su fadin albarkacin bakinsu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng