Tsohon Ɗan Majalisa Ya Danƙara wa Atiku Baƙaken Kalamai bayan Abin da Ya Faru a Taron BoT

Tsohon Ɗan Majalisa Ya Danƙara wa Atiku Baƙaken Kalamai bayan Abin da Ya Faru a Taron BoT

  • Tsohon ɗan majalisar tarayya, Hon. Tajudeen Yusuf ya ce girman kan Atiku Abubakar da sakacinsa ne suka jawowa PDP faɗuwa a 2023
  • Jigon PDP ya bayyana cewa Atiku ya ɗauka cewa babu makawa shi zai zama shugaban ƙasa na gaba a 2023 tun kafin a kaɗa ƙuri'a
  • Tajudeen ya yi ikirarin cewa duk rigimar da ake yi a PDP ƴan jam'iyyar ne ke kitsa ta saboda suna son cimma wasu buriksnsu a siyasa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Yayin da rikicin PDP ke kara tsananta, tsohon dan majalisar wakilai kuma jigo, Tajudeen Yusuf, ya dora alhakin faduwar jam’iyyar a zaben shugaban kasa na 2023 kan Alhaji Atiku Abubakar.

Hon. Tajudeen ya ce tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya nuna girman kai kuma ya ba kansa tabbacin cewa shi ne zai zama shugaban kasa, wanda hakan ya sa PDP ta sha kaye.

Kara karanta wannan

"Baki ke yanka wuya," Atiku Abubakar ya jawo wa kansa abin magana kan 'batun N50m'

Atiku da kusoshin PDP.
Rikicin PDP: Tsohon ɗan Majalisar Tarayya ya ce Atiku ya jawo wa kansa rashin nasara a 2023 Hoto: PDP Nigeria
Asali: Facebook

PDP ta kama hanyar maimaita kuskurenta a 2027

Jigon PDP ya bayyana hakan ne yayin da yake tsokaci kan tashin hankalin da ya nemi tarwatsa taron Kwamitin Amintattu (BoT) a Abuja a ranar Laraba, rahoton Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon ɗan Majalisar wakilan tarayyar ya ce idan ba a yi taka-tsan-tsan ba, PDP na iya maimaita kuskuren da ta yi a zaɓen da ya gabata a 2027.

A cewarsa, rikicin da ke ci gaba da addabar PDP yana da nasaba da yunkurin wasu jiga-jigan jam’iyyar da ke son karbe iko domin tsayawa takara a zaben 2027.

Tajudeen ya danƙarawa Atiku maganganu

"Abin da ke faruwa kafin 2027 shi ne wasu daga cikinmu suna kokarin kafa tsarinsu, sannan su samu ƙarfin iko da jam’iyya domin neman takara.
"Amma suna mantawa da cewa kasancewa dan takara kadai ba zai sa ka zama shugaban kasa ba. Mun sha kaye a zaben da ya gabata ne saboda dan takararmu ya cika girman kai kuma ya yi imanin cewa shi ne zai lashe zabe," in ji shi.

Kara karanta wannan

'Talauci ne': Ministan Buhari ya fadi dalilin shiga siyasa, ya bugi kirji kan kafa APC

PDP ta gaza a matsayin jam'iyyar adawa

Tsohon dan majalisar ya kuma caccaki PDP, yana mai cewa jam’iyyar ta gaza a matsayinta na babbar jam'iyyar adawa.

"PDP na cikin matsala saboda tana fama da mutane masu tsananin kwaɗayin mulki. Wasu ‘yan jam’iyya sun dauka cewa dole ne su tsaya takara a kowane zabe.
"Amma jam’iyya ba ta kasancewa ta wani mutum daya ba, ya kamata a samu ingantacciyar siyasa a ciki," in ji shi.

Wani ɗan PDP, Umar Idris, ya shaidawa Legit Hausa cewa tabbas idan ba a yi da gaske ba, jam'iyyar za ta maimaita kuskuren da ta yi a zaɓen 2023 da ya gabata.

A cewarsa, ba wai Atiku kaɗai ba, galibin shugabannin PDP na ƙasa da wasu gwamnoni sun taka rawa wajen kayar da jam'iyyar a 2023.

"Har yanzu idan na tuna zaɓen 2023 da halin da muke ciki na kan ji takaici, Atiku da Obi duk abu ɗaya ne, sune ƴan takarar PDP a 2019, me ya sa suka rabu a 2019?

Kara karanta wannan

'Ban son belin': Sowore ya buga da 'yan sanda, ya ce ya fi Tinubu karfin iko a baya

"Saboda haka kamar yadda ya fada, wallahi idan PDP ba ta yi da gaske ba, kashi za a sake ba ta a zaɓen 2027," in ji Umar.

Shugaban BoT ya nemi a kira taron NEC

A wani labarin, kun ji cewa shugaban BoT na ƙasa, Sanata Adolphus Wabara ya ce lokaci ya yi da PDP za ta shirya taron kwamitin zartarwa watau NEC.

Wabara ya ce duba da rikicin shugabancin da ke faruwa, mafita ɗaya da ta rage shi ne taron NEC domin raba gardama.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

iiq_pixel