Bayan Sukar APC, El Rufai Ya Yi Magana kan Shirinsa Na Barin Jam'iyyar

Bayan Sukar APC, El Rufai Ya Yi Magana kan Shirinsa Na Barin Jam'iyyar

  • Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufai ya yi magana kan rahotannin da ake yaɗawa na cewa yana shirin barin jam'iyyar APC
  • Nasir El-Rufai ya bayyana cewa ko kaɗan ko kaɗan bai da shirin barin jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya da ya yi gwamna har sau biyu a ƙarƙashinta
  • Malam El-Rufai ya bayyana cewa yana matsawa jam'iyyar APC ne saboda yana so ta gyara yadda take gudanar da harkokinta a ƙasar nan

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya yi magana kan jitar-jitar da ake yaɗawa ta shirinsa na ficewa daga jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya.

Nasir El-Rufai ya ƙaryata jita-jita da ke yawo a wasu kafafen sadarwa, wacce ke cewa yana shirin barin jam’iyyar APC.

El-Rufai ya musanta shirin barin APC
El-Rufai ya ce ba zai bar APC ba Hoto: Nasir El-Rufai
Asali: Facebook

El-Rufai ya bayyana hakan ne lokacin da yake magana da manema labarai ranar Talata a wurin babban taron ƙasa da aka kammala a birnin tarayya Abuja, cewar rahoton jaridar Vanguard.

Kara karanta wannan

APC ta yi martani bayan El Rufa'i ya kwance mata zani a kasuwa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Nasir El-Rufai ya musanta shirin barin APC

Tsohon gwamnan na jihar Kaduna ya bayyana cewa yana matsawa jam’iyyar APC lamba ne domin ta yi abin da ya dace.

“Ba zan bar APC ba. Ba ni da irin wannan shirin."

- Nasir Ahmad El-Rufai

Da aka tambaye shi dalilin da ya sa yake matsawa jam’iyyar lamba, sai ya kada baki ya ce:

"A’a, a’a, ina so ne su gyara."

A ranar Litinin, an ruwaito tsohon gwamnan na Kaduna yana sukar jam’iyyarsa ta APC, inda ya zarge ta da watsi da tsarinta na asali tare da samar da shugabanci mara inganci.

An samo mafita ga dimokuraɗiyyar Najeriya

A halin da ake ciki, domin ƙarfafa dimokuraɗiyya a Najeriya, taron ya ba da shawarar cewa dukkan jam’iyyun adawa su haɗu su samar da wata haɗaka mai ƙarfi da za ta iya fuskantar jam’iyyar APC mai mulki, kafin zaɓen gama-gari na shekarar 2027.

Kara karanta wannan

APC ta yi kaca kaca da Atiku Abubakar, ta fadi wanda ke haddasa rikici a PDP

Haka kuma, taron ya ba da shawarar cewa hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta ba sabbin jam’iyyun siyasa damar yin rijista kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada.

Karanta wasu labaran kan El-Rufai

Kotu ta hana jami'in gwamnatin El-Rufai beli

A wani labarin kuma, kun ji cewa wata babbar kotun jihar Kaduna ta ƙi yarda da buƙatar tsohon kwamishinan kuɗi na gwamnatin Nasir Ahmad El-Rufai, beli.

Kotun ta umarci a maida Alhaji Bashir Sa'idu gidan gyaran hali kan zarge-zargen da ake yi masa na almundahana da satar kuɗaɗen jama'a.

Alƙalin kotun mai shari'a Isa Aliyu ya ɗage shari’ar zuwa ranar 23 ga Janairu, 2025 don sauraron buƙatar belin da tsohon kwamishinan kuɗin ya gabatar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

iiq_pixel