"Ban Ƙwallafa Rai ba": Peter Obi Ya Canja Shawara kan Kudurin Zama Shugaba Ƙasa

"Ban Ƙwallafa Rai ba": Peter Obi Ya Canja Shawara kan Kudurin Zama Shugaba Ƙasa

  • Peter Obi ya ce bai wani kwallafa rai a kan lallai sai ya zama zama shugaban kasa ba, sai dai yana kwadayin ganin Najeriya ta gyaru
  • Tsohon dan takarar shugaban kasar ya bukaci matasa da su taimaka wajen samar da shugabancin da zai kawo gyara a kasar
  • Obi ya jaddada cewa Najeriya tana da damar ci gaba amma tana kin yin abin da ya dace, don haka ake bukatar jajurtattun shugabanni

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Amurka - Tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi, ya bayyana cewa bai ƙwallafa rai a kan sai ya zama shugaban kasar Najeriya ba.

Peter Obi ya bayyana hakan ne a wajen bikin yaye daliban makarantar jami'ar Nexford dake kasar Amurka.

Peter Obi ya yi magana kan kwallafa ran da ake cewa yana yi na zama shugaban kasa
Peter Obi ya yiwa masu cewa ya kwallafa ran zama shugaban kasa martani. Hoto: @PeterObi
Asali: Facebook

Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar LP a zaben 2023, ya ce shugabanci a Najeriya na wahalar da mutane, inji rahoton The Cable.

Kara karanta wannan

'Na samu lafiya,' Buhari ya fadi kalubalen da ya fuskanta a lokacin mulkinsa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Peter Obi ya magantu kan zama shugaban kasa

Peter Obi ya bukaci matasa da suka kammala karatu da su sanya sadaukarwa a gaba ga bukatun kawunansu domin kawo sauyi a Najeriya.

Ya kara da cewa,

“Abin da nake so shi ne ganin Najeriya ta samu ci gaba, ta hau turba mai kyau.
"Duka wadannan abubuwan da muke fada, muna fadinsu ne domin ku yi amfani da su ku kawo sauyi. Ba wai ku fara cewa 'ina son na zama mai iko. Ina so na yi wannan, ko na yi wancan.
"Idan mutane suna cewa na matsu, sai in ce masu a'a. Ni ban kwallafa ran sai na zama shugaban Najeriya ba. Na matsu naga Najeriya ta saitu."

Peter Obi ya ba matasa shawara

Obi ya ce dole ne matasan Najeriya su taimaka wajen samar da shugabancin da ya dace wanda zai kawo ci gaba a kasar.

Tsohon dan takarar shugaban kasar ya tuno da maganar marubuci James Robinson da ya ce Najeriya ta san abin da za ta yi ta samu ci gaba amma taki ta yi hakan.

Kara karanta wannan

Rikicin Tinubu da gwamnan Bauchi: Minista ya fadi dalilin rashin jituwa

Ya yi kira ga daliban da aka yaye da:

“Ku yi amfani da ilimin da kuka samu wajen taimakawa sauya al’umma. Kada ku zama wani bangare na wannan tsarin da bai son ci gaban kasa.”

Peter Obi ya zo na uku a zaben shugaban kasar Najeriya da aka gudanar a shekarar 2023 wanda ya fitar da Bola Ahmed Tinubu a matsayin shugaba.

Peter Obi ya shirya yin ritaya daga siyasa

A wani labarin, mun ruwaito cewa tsohon dan takarar shugaban kasa, Peter Obi, ya ce yana shirin komawa Onitsha don zama malami domin karfafa gwiwar ɗalibai.

Obi ya tallafa wa asibitin misiya a jihar Anambra da Naira miliyan 25, wanda ya haɗa da gudunmawar da ya bayar lokacin da yake gwamna.

Tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi, ya bayyana shirinsa na yin ritaya daga siyasa tare da mai da hankali kan ayyukan tallafa wa al’umma.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.