Rigima Ta Dawo Ɗanya, Shugaban PDP na Ƙasa Zai Sauka daga Mukaminsa a Karshen 2025

Rigima Ta Dawo Ɗanya, Shugaban PDP na Ƙasa Zai Sauka daga Mukaminsa a Karshen 2025

  • Mataimakan shugabannin PDP na ƙasa sun haɗa kai, sun ayyana cikakken goyon bayansu ga mukaddashin shugaban jam'iyya, Umar Damagum
  • Timothy Osadolor, mataimakin shugaban matasan PDP ya ce Damagum ba zai sauka daga shugabanci ba har sai wa'adi ya ƙare a watan Disambar 2025
  • Ya kuma bayyana cewa Samuel Anyanwu ne halastaccen sakataren PDP na ƙasa har sai kotu ta yanke hukuncin da ya saɓawa hakan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Rigimar da ke faruwa a babbar jam'iyyar adawa watau PDP ta sake buɗe sabon shafi a ranar Laraba, 22 ga watan Janairu, 2025.

Mataimakan shugabannin jam'iyyar na ƙasa sun ayyana cikakken goyon bayansu ga mukaddashin shugaban PDP na ƙasa, Ambasada Umar Damagum.

Umar Damagum.
Wasu yan NWC sun ja daga, sun ce Damagum ba zai sauka daga kujerar shugaban PDP ba Hoto: @OfficialPDPNig
Asali: Twitter

A cewarsu, Damgum wanda ke jagorantar kwamitin gudanarwa na ƙasa (NWC) na nan daram a kujerarsa har karshen 2025, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

'Buhari ya nuna rashin gamsuwa da mulkin Bola Tinubu,' PDP ta tono magana

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yaushe shugaban PDP na ƙasa zai sauka?

Sun kuma yi kira ga sauran mambobin NWC da ke adawa da Damagum da su daina ɓata sunan jam'iyyar ta hanyar sukar mukaddashin shugaban.

A cewar mataimakan shugabannin PDP, ba za a iya cire Damagum ba har sai wa'adin NWC ya ƙare a watan Disambar 2025.

Mataimakin shugaban matasan PDP na ƙasa, Timothy Osadolor ne ya bayyana hakan a madadin sauran mataimakan a wata hira da manema labarai a hedkwatar jam'iyyar.

PDP a Arewa ta Tsakiya na kan bakarta

Wannan dai na zuwa ne yayin da ƴan PDP a shirryar Arewa ta Tsakiya ke ci gaba da matsa lamba kan a dawo ma yankin kujerar shugaban jam'iyyar.

Sum yi ikirarin cewa a tanadin kundin tsarin mulkin PDP, ya zama wajibi a bar yankin ya kammala wa'adin Iyorchia Ayu.

Da ƴake zantawa da ƴan jarida jiya Laraba, Osadolor ya ce wa'adin Damagum bai ƙare ba har zuwa Disamba 2025.

Kara karanta wannan

Mawaki Rarara ya rikita taro da gwamna ya kaddamar da yakin neman zabe a Katsina

Ya yi kira ga mambobin da ke ɓata sunan jam'iyyar da su daina, su ba Damagum damar sake gina PDP.

Rigima kan kujerar sakataren PDP

Dangane da rigima kan kujerar sakatare na ƙasa tsakanin Samuel Anyanwu da Sunday Ude-Okoye, Osadolor ya ce batun na gaban kotu.

Sai dai ya ƙara da cewa Sanata Samuel Anyanwu ne sakataren PDP a yanzu har sai kotu ta yanke hukunci akasin haka.

Ya kuma yi kira ga 'ya'yan jam'iyyar da su haɗa kai wuri guda kuma su yi aiki tuƙuru don mayar da PDP kan mulki a 2027, Vanguard ta kawo.

Timothy Osadolor ya nanata cewa kwamitin gudanarwa NWC ya shirya tsaf wajen ganin PDP ta dawo kan turba domin tunkarar zaɓuka masu zuwa.

Wani jigon PDP kuma ɗaya daga cikin shugabanni a Ɗanja, jihar Katsina, Muazu Rabiu ya shaidawa Legit Hausa cewa jam'iyyar tana fuskantar lokaci mai sarƙaƙiya.

Ya ce zabe mai zuwa dama ce ga PDP to amma rikicin cikin gidan da ke faruwa ka iya sake durƙusar da jam'iyyar.

Kara karanta wannan

Buhari, Radda da manyan 'yan siyasa sun yi taron neman nasara ga APC

"Muna buƙatar taron majalisar zartarwa na ƙasa watau NEC don warware taƙaddamar shugabancin PDP idan ba haka ba, bana tunanin za a warware rikicin nan kusa.
"Idan ka duba halin da ƴan ƙasa ke ciki, PDP na da babbar dama a 2027, amma wannan rikicin zai iya ƙara ƙayar da ita kamar dai yadda ya faru a 2023," in ji shi.

Sanatan Delta ya sauya sheka zuwa APC

A wani labarin, kun ji cewa Sanata Ned Nwoko daga jihar Delta a kudancin Najerirya ya sanar da ficewarsa daga PDP zuwa jam'iyyar APC.

Wannan sauya sheƙa dai ta sa APC kwace dukkan kujerun sanatoci uku na jihar Delta, lamarin da ake ganin barazana ce ga jam'iyyar PDP mai mulki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262