Bafarawa: Tsohon Gwamnan Jihar Sokoto Ya Fice daga Jam'iyyar PDP, Ya Fadi Dalili
- Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Attahiru Bafarawa, ya fice daga PDP, inda ya bayyana ƙudurinsa na bude sabon babi na rayuwa
- Wasiƙar ficewar Bafarawa ta fito ne a daidai lokacin da PDP ke fama da rikicin shugabanci da rashin haɗin kai a cikin jam'iyyar
- Masana dai na ganin watakila jam'iyyar PDP na iya kara rage karsashi a idon 'yan Arewa maso Yamma, musamman a jihar da ya fito
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Sokoto - Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Dalhatu Attahiru Bafarawa, ya sanar da ficewar sa daga babbar jam'iyyar adawa ta Najeriya, watau PDP.
Wannan sanarwa ta fito ne cikin wata wasiƙa wadda ya sanya wa hannu da kansa, kuma ta ɓulla a ranar Talata, 14 ga watan Janairu, 2025.
Jaridar BBC Hausa ta rahoto cewa Bafarawa ya sanar da ficewarsa ne a cikin wasiƙar da ya rubuta wa shugaban jam'iyyar PDP na ƙasa a ranar 8 ga watan Janairu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bafarawa ya fice daga jam'iyyar PDP
A cikin wasikar, Attahiru Bafarawa ya bayyana cewa ya yanke wannan shawara ne tare da ƙudurin gina sabon babi a rayuwarsa.
Tsohon gwamnan ya ce:
"Na rubuto wannan takarda domin gabatar da matakin ficewa ta daga jam'iyyar PDP."
Bafarawa ya bayyana cewa shawarar ficewarsa ba mai sauƙi ba ce, amma ya ɗauke ta ne domin mayar da hankali kan wasu sabbin tsare-tsare da suka dace da burinsa na bunƙasa al'umma.
Ya ce burinsa shi ne ya ba matasa damar samun cigaba ta hanyar sabbin dabaru.
Matsaloli sun yiwa jam'iyyar PDP katutu
Wannan mataki na tsohon gwamnan ya zo a daidai lokacin da PDP ke fama da rikice-rikicen cikin gida, musamman na shugabanci da rashin jituwa tsakanin manyan ƴan jam'iyyar.
Kwana guda kafin bayyana ficewar Bafarawa, wasu ƴan jam'iyyar sun gudanar da zanga-zanga a babban ofishin PDP da ke Abuja.
Zanga-zangar ta samo asali ne daga rikici kan sahihin sakataren jam'iyyar na ƙasa, wanda ya jawo ce-ce-ku-ce.
Tun bayan rushewar gwamnatinta a shekarar 2015, PDP ta sha fama da matsaloli daban-daban, ciki har da ƙarancin haɗin kai daga shugabanni daga yankuna daban-daban na ƙasar.
Wannan rashin jituwa ya yi sanadin koma baya wajen tafiyar da ayyukan jam'iyyar.
Tasirin ficewar Bafarawa daga jam'iyyar PDP
Ficewar Bafarawa daga PDP ta ƙara nuna yadda lamurra suka dagulewa jam'iyyar adawar.
Ana kuma ganin hakan na iya rage wa jam’iyyar tasiri a Arewa maso Yamma, inda tsohon gwamnan ya ke da rinjaye.
A gefe guda, masana harkokin siyasa suna ganin cewa matakin tsohon gwamnan zai iya zama jigon sake fasalin siyasar PDP a yankinsa.
Sai dai kuma, har yanzu ba a san jam’iyyar da zai koma ba, ya bar magoya bayansa a cikin duhu.
Bafarawa ya ba al'ummar Sokoto kyautar N1bn
A wani labarin, mun ruwaito cewa tsohon gwamnan Sokoto, Attahiru Bafarawa, ya tallafa wa al'ummar jiharsa da Naira biliyan ɗaya domin rage radadin talauci.
Rahotanni sun tabbatar cewa gidauniyar Attahiru Bafarawa ce ta shirya taron da ya ba da damar bai wa al'umma wannan tallafi mai muhimmanci.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng