'Ba Kwankwaso ba ne': Gwamna Abba Ya Fadi Wanda Ya Jefa 'Yan Kano a Wahalar Rayuwa
- Gwamna Abba Yusuf ya zargi Abdullahi Umar Ganduje da jefa tsofaffin ma'aikatan jihar Kano cikin matsananciyar wahala
- Mai girma Abba ya ce Ganduje ya sauka ya bar hukumar fansho da bashin sama da Naira biliyan 48 na hakkokin tsofaffin ma'aikata
- A hannu daya, Gwamna Abba ya cika alkawarinsa na biyan hakkokin fansho, inda aka saki Naira biliyan 16 ga ma’aikata 6,886
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kano - Gwamna Abba Yusuf ya zargi shugaban APC na kasa, Abdullahi Ganduje, da jefa 'yan fansho a mawuyacin hali yayin mulkinsa na shekaru takwas.
Mai girma Abba ya ce Ganduje bai bai wa fansho da hakkokin tsofaffin ma’aikatan Kano muhimmanci ba, yana mai bayyana yadda ya bar bashi mai yawa.
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Abba ya zargi Ganduje da kin biyan fansho
Sanarwar ta ce Abba ya koka kan yadda gwamnatin baya ta yi watsi da biyan kudaden fansho tsawon shekaru takwas, inda bashin ya kai fiye da Naira biliyan 48.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis, yayin kaddamar da biyan Naira biliyan biyar na hakkokin ma’aikata da fansho a gidan gwamnatin Kano.
A cikin sanarwar, Gwamna Yusuf ya tausaya wa 'yan fansho da suka sha wahala saboda gazawar gwamnatin Ganduje.
Mai girma Abba ya jaddada cewa daruruwan 'yan fansho sun rasa rayukansu yayin da suke jiran hakkokinsu da aka hana su ba tare da wani dalili ba.
Abba ya fara gyara kuskuren Ganduje
Gwamna Abba ya ce:
"Gwamnatin Ganduje ta yi sakaci wajen biyan hakkokin ma’aikata tsawon shekaru takwas, lamarin da ya jefa 'yan fansho cikin wahala a Kano."
"Wannan ita ce babbar matsalar matsalar kin biyan hakkokin tsofaffin ma'aikata da aka taba gani tun kafa jihar Kano a 1967."
Domin ganin cewa bai bi sahun magabacinsa ba, Abba ya raba Naira biliyan 16 ga tsofaffin ma'aikata ma’aikata 6,886 cikin matakai uku don biyan bashin hakkokinsu.
Tsarin gwamnatin Abba na biyan kudin fansho
Yusuf ya ce biyan hakkokin ma’aikata ba wai tilas ne kawai ba, wani nauyi ne da kowane shugaba ya kamata ya sauke.
Ya tabbatar wa 'yan fansho cewa za a bi matakan da za su tabbatar da gaskiya wajen biyansu hakkokinsu, ta hanyar tura kudade kai tsaye ga asusunsu daga baitul mali.
Gwamnan ya umarci da a nemo 'yan uwan wadanda suka rasu domin tabbatar da biyan Naira miliyan 846 na hakkokin da ba a karba ba.
Abba ya karawa 'yan fansho albashi
Abba ya ce biyan Naira biliyan shida ga ma’aikata 2,667 shi ne mataki na farko, sannan aka saki Naira biliyan 5 ga ma’aikata 2,216 a mataki na biyu.
"A yau, ina cikin farin ciki na kaddamar da mataki na uku na biyan Naira biliyan biyar ga tsofaffin ma’aikata 2,000."
Gwamnan ya kuma sanar da karin mafi karancin kudin fansho daga N5,000 zuwa N20,000 domin saukaka tasirin hauhawar farashi.
Kano: An yi taron biyan hakkokin 'yan fansho
Tun da fari, mun ruwaito cewa mai girma gwamnan Kano, Abba Yusuf ya yi gagarumin taron biyan hakkokin tsofaffin ma'aikatan jihar a gidan gwamnati.
Gwamna Abba ya jaddada aniyarsa ta biyan dukkanin basussukan fansho da na giratuti da tsofaffin ma'aikatan jihar suke bi da ya kai Naira biliyan 48.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng