Dan Bilki Kwamanda: Abba Ya Hana Ni zuwa Aikin Hajji duk da Taimakon Kashim Shettima

Dan Bilki Kwamanda: Abba Ya Hana Ni zuwa Aikin Hajji duk da Taimakon Kashim Shettima

  • AbdulMajid Dan Bilki Kwamanda ya zargi gwamnan Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, da soke sunansa daga jerin masu tafiya aikin hajji
  • Kwamanda ya bayyana cewa Mataimakin Shugaban kasa, Kashim Shettima, ne ya ba shi damar tafiya, bayan gwamnan Kano ya hana
  • Kwamanda ya nuna takaicinsa kan yadda Mai girma gwamnan Kano ya cire sunansa daga cikin wadanda za su yi hajjin a shekarar 2023

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Jigo a jam’iyyar APC, reshen jihar Kano, AbdulMajid Dan Bilki Kwamanda ya zargi gwamnan Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf da soke sunansa daga cikin masu zuwa aikin hajji.

A wata hira da ya gabatar, Dan Bilki Kwamanda ya bayyana cewa babu ko sisinsa a aikin hajjin da gwamnan Kano ya haramtawa masa zuwa bayan hawan mulkin gwamnatin Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

APC: El Rufa’i ya bayyana matsayinsa kan jita jitar sauya sheka

Kwamanda
Kwamanda ya zargi gwamnan Kano da shiga hakkinsa Hoto: AbdulMajeed Mustapha Kwamanda/Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

A bidiyon da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Dan Bilki Kwamanda ya bayyana cewa mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ne ya biya masa kujerar aikin hajji a shekarar da ta gabata watau 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana cewa a wannan lokacin ne gwamnati ta kwace fasfo dinsa, bayan ya kammala biya wa iyalansa kudin aikin hajji don sauke farali a kasa mai tsarki, lamarin da ya ce bai dace ba.

Zargin Kwamanda a kan gwamnan Kano

AbdulMajid Danbilki Kwamanda, masoyi ga tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bayyana cewa ya yi takaicin tsige sunan shi da gwamnan Kano ya yi.

Ya bayyana cewa Injiniya Abba Kabir Yusuf ya ga sunansa a cikin wandanda Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya yi ba damar ziyartar kasa mai tsarki.

Ya ce;

"Wannan hajjin ma, Mataimakin shugaban kasa ya ba ni kujera, da Abba ya ga sunana sai ya soke.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya ziyarci IBB, ya bayyana abubuwan da suka tattauna a kan Najeriya

Waccan hajjin ma. Waccan hajjin ma da kudina, da wannan hajjin da mataimakin shugaban kasa ya ba ni kujerar, ban taba fada sai yau don na yi wa Lamin alkawarin ba zan ci mutuncin ma'aikatarsa ba."

Kwamanda ya wanke hukumar hajji

Bayan ya zargi gwamnatin Kano da soke sunan shi daga cikin jerin wadanda aka yi wa alkawarin zuwa aikin hajji, ya wanke hukumar.

A cewar 'dan siyasar, babu mamaki wasu manya ne suka ba Lamin Danbappa wannan umarni na haka shi sauke farali kamar yadda ya saba.

AbdulMajid Dan Bilki Kwamanda ya kara da cewa;

"Magana ce ta zo, ba wai don tozarwa ko cin mutunci ba. Shi kansa na san ba wai lallai halinsa ba ne, kila halin Ogansa ne."

Jami'ai sun zane Kwamanda a Kaduna

A baya, mun ruwaito cewa an gano wani bidiyo da ya yi fice a Kaduna, an ga wani mutum da abokansa suna dukan masoyin tsohon shugaban kasa, AbdulMajeed Dan Bilki Kwamanda.

Kara karanta wannan

'Ni jan biro ne maganin dakikin yaro,' Gwamna Fubara ya jijjige Wike da mutanensa

Wannan lamarin ya faru ne bayan an zargi Kwamanda da zagin Gwamnan Kaduna, Uba Sani, lamarin da ya jawo cece-kuce a kafafen sada zumunta, inda jama'a suka bayyana rashin jin dadi.

A bangarensa, AbdulMajid Dan Bilki Kwamanda ya bayyana cewa babu kamshin gaskiya a cikin zargin da aka rika yi masa, ya ce ya na da 'yancin fadin albarkacin bakinsa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.