LND: Ana Shirin Kafa Sabuwar Jam'iyya domin Buga APC da Kasa a 2027

LND: Ana Shirin Kafa Sabuwar Jam'iyya domin Buga APC da Kasa a 2027

  • Kungiyar League of Northern Democrats (LND) karkashin jagorancin Sanata Ibrahim Shekarau na shirin sauyawa zuwa jam'iyyar siyasa kafin zaben 2027
  • LND ta zargi jam'iyyun APC da PDP da gazawa wajen cika burin 'yan Najeriya, tana neman hadin gwiwa da kungiyoyin siyasa daga Kudu domin kafa jam'iyya mai karfi
  • APC ta mayar da martani cewa wannan ba zai zama barazana ga nasarar ta a zaben 2027 ba, tana mai jaddada cewa manufofinta suna haifar da sakamako mai kyau

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Kungiyar League of Northern Democrats (LND) karkashin jagorancin tsohon gwamnan Kano, Sanata Ibrahim Shekarau, ta bayyana shirinta na sauyawa zuwa jam'iyyar siyasa.

LND ta yi wannan yunkuri ne domin cika burin 'yan Najeriya da ke neman canji daga mulkin jam'iyyun APC da PDP.

Kara karanta wannan

Ganduje ya yi wa Kwankwaso shagube, ya yi barazanar kwace Kano a zaben 2027

Shekarau
Kungiyar shekarau za ta dawo jam'iyyar siyasa. Hoto: Ibrahim Shekarau
Asali: Facebook

Jairdar Daily Trust ta wallafa cewa bayanin ya fito ne a cikin wata sanarwar da daya daga cikin jagororin LND, Dakta Umar Ardo, ya fitar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kungiyar NLD za ta hada kai da 'yan Kudu

Tribune ta rahoto cewa LND na neman goyon bayan kungiyoyin siyasa daga Kudu domin kafa sabuwar jam'iyya mai karfi da za a buga da ita a zaben 2027.

Jagoran tafiyar ya zargi jam'iyyun APC da PDP da gazawa wajen magance matsalolin da suka addabi kasa, ciki har da talauci, rashin tsaro, da cin hanci.

Ardo ya ce,

"Shirin ya yi daidai da burin 'yan Najeriya da ke neman ficewa daga mulkin da bai cika musu buri ba na PDP da APC, musamman a Arewacin Najeriya."

Martanin APC kan kafa sabuwar jam'iyya

A martanin da ya mayar, Daraktan Yada Labaran APC, Alhaji Bala Ibrahim, ya ce shirin LND na sauyawa zuwa jam'iyyar siyasa ba zai zama barazana ga APC a zaben 2027 ba.

Kara karanta wannan

2027: Ana zargin wasu gwamnonin PDP da shirin sauya sheka zuwa APC

Ya bayyana zargin da ake yi wa jam'iyyar APC a matsayin marasa tushe, yana mai jaddada cewa manufofin APC suna haifar da sakamako mai kyau ga 'yan kasa.

LND ta yi kira ga 'yan Najeriya

Yayin da LND ta nemi hadin gwiwa da kungiyoyin siyasa daga Kudu domin kafa sabuwar jam'iyya a 2027, ta yi kira ga 'yan Najeriya.

Kungiyar ta bukaci 'yan Najeriya da su marawa wannan yunkuri baya domin samun canji a tsarin mulkin kasar.

Jam'iyyar APC ta ce za a zabe ta a 2027

Jam'iyyar APC ta bayyana cewa ba ta jin tsoron shirin LND na kafa sabuwar jam'iyya, tana mai cewa manufofinta suna samun karbuwa a wajen 'yan Najeriya.

Alhaji Bala Ibrahim ya ce APC na da mafi kyawun manufofi da tsare-tsare da za su amfanar da 'yan Najeriya kuma hakan zai ba su nasara a 2027.

Tattaunawar na zuwa ne ne a daidai lokacin da aka fara magana kan shirye-shiryen zaben 2027, inda kungiyoyi da jam'iyyun siyasa ke neman samun goyon bayan 'yan kasa.

Kara karanta wannan

APC: El Rufa’i ya bayyana matsayinsa kan jita jitar sauya sheka

NNPP ta ce Kwankwaso zai ci zaben 2027

A wani rahoton, kun ji cewa jam'iyyar NNPP ta ce 'yan Najeriya sun gaji da mulkin APC saboda matsalolin tattalin arziki da suka kawo.

Shugaban NNPP na jihar Kano ya bayyana cewa akwai alamu da suka nuna cewa magudun Kwankwasiyya, Rabi'u Kwankwaso zai lashe zabe a 2027.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng