Akpabio: Gaskiyar Abin da Ya Sa Shugaban Majalisar Dattawa Ya Sauya Sheka zuwa APC
- Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya ce APC za ta lashe dukkanin jihohin Kudu maso Kudu a zaɓen 2027
- Akpabio ya ce zaɓen Monday Okpebholo a matsayin gwamnan Edo ya kasance hukuncin Allah don kawo sauƙi ga jama’ar jihar
- Shugaban majalisar ya bayyana dalilin da ya sa ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC da kuma kokarinsa ga yankin Kudu
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Uyo - Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya ce jam’iyyar APC za ta lashe dukkanin jihohin Kudu maso Kudu a zaɓen 2027.
Akpabio ya bayyana zaɓen Sanata Monday Okpebholo a matsayin Gwamnan Edo a matsayin hukuncin Allah na kawo sauƙi ga jama’ar jihar.
Akpabio ya fadi jihohin da APC za ta kwace
Shugaban majalisar ya yi wannan bayani ne a karshen mako yayin da Gwamna Okpebholo ya ziyarce shi a Uyo, babban birnin Akwa Ibom a cewar rahoton Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jaridar Legit.ng Hausa ta fahimci cewa daga cikin jihohin Kudu maso Kudu guda shida, APC tana mulki a Edo da Cross River kawai.
Jam’iyyar PDP tana mulki a jihohi hudu na yankin – Akwa Ibom, Rivers, Bayelsa da kuma Delta.
Dalilin da ya sa Akpabio ya koma APC
Akpabio ya bayyana cewa ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC ne domin ganin cewa yankin Kudu maso Kudu ya shiga cikin harkokin siyasar ƙasar.
Shugaban majalisar dattawan ya ce:
“Mun yanke shawarar canja jam’iyyar siyasa domin mu wakilci mutanenmu yadda ya kamata a matakin ƙasa.”
Akpabio ya kara da cewa APC tana kan hanyar samun karin jihohi a yankin bisa dukkanin alamu na siyasa.
Dalilin Gwamna Okpebholo na ziyartar Akpabio
Shugaban majalisar ya kuma nuna fatan cewa kwace wadannan jihohin zai kawo sauyi mai kyau ga ci gaban yankin Kudu maso Kudu.
A nasa ɓangaren, Gwamna Okpebholo ya ce ya ziyarci Akwa Ibom ne don koyon dabaru daga shugabansa Akpabio.
“Na zo neman shawararsa da koyo daga gogewarsa, kuma ya yi farin ciki da gani na tare da ba ni shawarwari masu muhimmanci."
- A cewar Okpebholo.
Akpabio ya gano bara-gurbi a ministocin Tinubu
A wani labarin, mun ruwaito cewa sugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya nemi shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi kaffa kaffa da wasu ministocinsa.
Sanata Akpabio ya bayyana cewa wasu ministoci a gwamnatin Tinubu suna bijirewa umarnin majalisar tarayya idan ta bukaci ganinsu wanda ya sabawa doka.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng