'Lokacin ba Su Dama Ya Yi': Fasto Ya Yi Adalci, Ya Bukaci ba Musulmi Damar Mulkin Jiha

'Lokacin ba Su Dama Ya Yi': Fasto Ya Yi Adalci, Ya Bukaci ba Musulmi Damar Mulkin Jiha

  • Yayin da Kiristoci za su shafe shekaru 12 zuwa 2027 suna mulkin Lagos, an bukaci ba Musulmai dama domin rike muƙamin
  • Fasto Isaac Ayo Olawuyi shi ya yi wannan roko domin yin adalci da kula da hakkokin addini musamman a bangaren mulki
  • Kafin shekaru 12 na mulkin Kiristoci, Musulmai sun mulki jihar daga 1999 zuwa shekarar 2015

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Lagos - Shugaban Cocin Methodist a Najeriya, Rabaran Isaac Ayo Olawuyi ya magantu kan siyarar jihar Lagos.

Rabaran Olawuyi ya ce ya kamata a zabi gwamnan jihar Musulmi a zaben 2027 bayan kammala mulkin Babajide Sanwo-Olu.

Fasto ya bukaci ba Musulmai damar mulkin Lagos
Wani Fasto a Lagos ya ce lokaci ya yi da ya kamata Musulmi su karbi ragamar mulkin jihar. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu, Babajide Sanwo-Olu.
Asali: Facebook

Tarihin Mulkin Lagos: Kiristoci da Musulmai

Olawuyi ya bayyana haka ne yayin bikin godiya na shekara-shekara karo na 22 a Lagos, cewar rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

'Arewa na fushi da kai': an gargadi Tinubu ya gyara tafiyarsa, yankin na neman mafita

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Akinwunmi Ambode da Gwamna Babajide Sanwo-Olu, dukansu Kiristoci ne, kuma za su kammala mulkin shekaru 12 a Lagos zuwa 2027.

Sanwo-Olu zai kammala zangonsa na biyu na shekaru takwas a matsayin gwamna, yayin da Ambode ya yi shekara hudu kacal tsakanin 2015 da 2019.

Tun daga 1999 zuwa 2015, Bola Ahmed Tinubu da Babatunde Fashola dukansu Musulmai sun shugabanci jihar a matsayin gwamnoni.

Fasto ya bukaci ba Musulmai dama a Lagos

Olawuyi ya ce zuwa shekarar 2027 zai cika shekaru 12 da Kiristoci ke mulki a matsayin gwamnoni ba tare da ba Musulmi dama ba.

Fasto Olawuyi ya bukaci a yi la'akari da addini musamman zuwa zaben 2027 bayan shekaru 12 na mulkin Kiristoci, cewar Daily Post.

“Dole ne mu yi la’akari da addini a jihar Legas zuwa 2027 za mu cika shekaru 12 muna da Kiristoci a matsayin gwamnoni."
"Yanzu lokaci ya yi da za a ba ‘yan uwanmu Musulmi damar mulkarmu a Lagos."

Kara karanta wannan

Gwamna na kuntatawa 'yan majalisu masoyan tsohon gwamna? hadiminsa ya magantu

“Muna addu’ar cewa lokacin zabe zai kasance dama ta musamman wajen zaben wanda zai jagorance mu cikin nasara a Lagos."

- Isaac Ayo Olawuyi

Gwamna Sanwo-Olu zai wadata Lagos da abinci

Kun ji cewa yayin da yan Najeriya ke cigaba da kokawa kan halin da ake ciki, Gwamnatin Lagos ta dauko hanyar dakile hakan.

Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya shirya samar da shinkafa a kasuwannin jihar domin karya farashi ga al'umma.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.