'Sun Fara Shirin Murde Zabe' Farfesa Jinadu Ya Tono Zargin Magudi a 2027

'Sun Fara Shirin Murde Zabe' Farfesa Jinadu Ya Tono Zargin Magudi a 2027

  • Farfesa Adele Jinadu ya yi zargin cewa jagororin siyasar ƙasa sun fara shirye-shiryen magudin zaɓen 2027 mai zuwa
  • Adele Jinadu ya yi zargin cewa sayen ƙuri'u da tikitin takara sun zama ruwan dare maimakon tabbatar da gaskiya a lokacin zaɓe
  • Ya yi kira ga 'yan Najeriya da su tashi tsaye wajen yaƙi da cin hanci da rashawa da kuma neman gyara tsarin shari'a

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Masanin kimiyyar siyasa, Farfesa Adele Jinadu ya yi zargin cewa 'yan siyasar Najeriya sun fara shirin magudin zaɓen 2027.

Farfesa Adele Jinadu ya ce hakan na faruwa ne yayin da ake naɗa mutane masu goyon bayan jam'iyyu a hukumar INEC.

Mahmud Yakubu
An zargi 'yan siyasa da shirya magudin zabe a 2027. Hoto: INEC Nigeria
Asali: Twitter

Farfesa yana zargin za a murde zabe

Vanguard ta wallafa cewa ya yi jawabin ne yayin magana a taron tattaunawa kan yaƙi da cin hanci a Najeriya a Abuja a ranar Talata.

Kara karanta wannan

Jigo a NNPP ya yi martani kan bukatar 'yan Arewa su hakura da karawa da Tinubu a 2027

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Farfesa Jinadu ya ce nada 'yan siyasa a INEC na nuni da cewa za a ƙara kawo cikas ga adalci da gaskiya a tsarin zaɓe na ƙasa.

Ya ƙara da cewa a shekara mai zuwa, za a sabunta mukamin da yawa cikin kwamishinonin INEC kuma hakan zai bai wa shugabanni damar naɗa waɗanda za su yi musu biyayya.

Kalubalen yaƙi da cin hanci a Najeriya

Farfesa Jinadu ya ce tsoma bakin 'yan siyasa yana hana hukumomin EFCC da ICPC gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.

Ya yi nuni da cewa sauyawa da maida shugabannin hukumomin a kai-a kai yana kawo tangarda a aikin su, musamman ma EFCC da ta samu shugabanni tara tun kafuwar ta a shekarar 2003.

Jinadu ya yi kira a gyara tsarin shari'a na ƙasa domin magance cin hanci da rashawa yadda ya kamata a Najeriya.

Kara karanta wannan

Wani matashi ya daɓawa mahaifiyarsa wuƙa har lahira, ya ce ita ta hana shi arziƙi

APC ta ce Tinubu zai zarce a 2027

A wani rahoton, kun ji cewa APC ta bayyana cewa haɗin gwiwa tsakanin Atiku Abubakar da Peter Obi ba zai iya hana APC nasara a 2027 ba.

Daraktan yada labaran APC, Bala Ibrahim ya ce jam’iyyun adawa suna fama da rikici, kuma hakan zai hana su yin tasiri wajen kayar da APC.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng