Zaben 2027: Akume Ya ba Atiku da 'Yan Arewa Shawara kan Neman Kujerar Tinubu

Zaben 2027: Akume Ya ba Atiku da 'Yan Arewa Shawara kan Neman Kujerar Tinubu

  • Sakataren gwamnatin tarayya ya ba ƴan siyasan Arewacin Najeriya da su kawar da tunanin neman kujerar shugaban ƙasa a 2027
  • Sanata George Akume ya buƙaci Atiku Abubakar da ya haƙura da neman kujerar shugaban ƙasa a 2027 domin lokacin ƴan Kudu ne
  • Ya bayyana cewa ya kamata a bari shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya kammala wa'adinsa na biyu a shugabancin ƙasar nan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Sakataren gwamnatin tarayya (SGF), Sanata George Akume, ya ba ƴan siyasan Arewacin Najeriya shawara kan zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

George Akume ya buƙaci ƴan siyasar Arewa masu son tsayawa takarar shugabancin ƙasa a 2027, da su kawar da burinsu su jira har zuwa 2031 lokacin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kammala wa’adinsa na biyu.

Akume ya ba Atiku shawara
George Akume ya bukaci 'yan Arewa su hakura da takarar shugaban kasa a 2027 Hoto: @SGFAkume, @OfficialABAT, @atiku
Asali: Twitter

Sanata George Akume ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da tashar talabijin ta TVC a ranar Lahadi.

Kara karanta wannan

Tinubu ya kori shugaban hukuma kasa da awa 24 bayan bashi mukami

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sakataren gwamnatin tarayyar ya bayyana cewa har yanzu lokacin Kudancin Najeriya ne wajen samar da shugaban ƙasa a 2027.

Wace shawara Akume ya ba Atiku?

George Akume ya buƙaci tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, da ya kawar da tunanin shiga fadar Aso Rock Villa a matsayin shugaban ƙasa a shekarar 2027.

Ya ce idan Allah ya nufa ya zama shugaban ƙasa zai iya lashe zaɓe yana da shekaru 90 a duniya.

"Shugaba Tinubu a matsayinsa na ɗan Kudu ya kamata a bar shi ya yi wa'adi na biyu, hakan na nufin waɗanda ke son kujerar shugaban ƙasa daga Arewa a 2027, su haƙura su jira har sai 2031."
"Idan Allah ya nufa Alhaji Atiku Abubakar zai zama shugaban ƙasa, ko da yana shekara 90 ne, zai iya samu. Amma da shi da sauran ƴan Arewa da ke son kujerar su jira har sai bayan 2027."

- George Akume

Kara karanta wannan

Wike ya ba 'yan Najeriya shawara kan gwamnatin Bola Tinubu

Jigo a APC ya faɗi kuskuren Atiku da Obi

A wani labarin kuma, kun ji cewa wani jigo a jam'iyyar APC ya bayyana kuskuren da Atiku Abubakar da Peter Obi suka yi a zaben shugaban ƙasa na 2023.

Ismael Ahmed ya bayyana cewa rashin haɗewa waje ɗaya da ƴan siyasar suka yi, ya ba Shugaba Bola Tinubu damar lashe zaɓe.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng