'Gidan Yari Ya Sauya Ni' Hon. Farouk Lawan Ya Magantu, Ya Yabawa Siyasar Kwankwaso

'Gidan Yari Ya Sauya Ni' Hon. Farouk Lawan Ya Magantu, Ya Yabawa Siyasar Kwankwaso

  • Bayan fitowa daga gidan yari, tsohon dan Majalisar Tarayya daga jihar Kano ya fadi darasin da ya koya
  • Hon. Farouk Lawan ya ce zamansa a gidan gyaran hali na tsawon shekaru ya mayar da shi mutumin kirki
  • Tsohon dan Majalisar ya kuma bayyana matsayar siyasarsa inda ya yabawa tsarin Sanata Rabi'u Kwankwaso

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Tsohon dan Majalisar Tarayya daga jihar Kano, Farouk Lawan ya yi magana kan rayuwar da ya yi a gidan gyaran hali .

Lawan ya bayyana hukuncin daurin shekaru bakwai da aka yanke masa a matsayin wani darasi na rayuwa da kuma jarabawa ga rayuwarsa.

Tsohon Majalisar Tarayya a Kano ya yabawa tsarin siyasar Kwankwaso
Hon. Farouk Lawan ya jerk darussan da ya koya a gidan yari. Hoto: Hon. Farouk Lawan.
Asali: Facebook

'Darussan da na koya a gidan yari' - Farouk Lawan

Tsohon dan Majalisar ya fadi haka ne yayin wata ziyarar a mazabar Shanono/Bagwai da ke jihar, cewar Tribune.

Kara karanta wannan

Sokoto: Jigon PDP ya dauki nauyin kaciyar yara 1,000, an kwarara masa yabo

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lawan ya ce ya kai ziyarar ba domin siyasa ba illa ta'azziya da kuma jajantawa marasa lafiya.

Hon. Lawan ya kuma yi magana kan siyasa inda ya yabawa tsarin siyasar Sanata Rabi'u Kwankwaso da makomar siyasarsa.

“A yau, na zama mutum mafi kyau, kuma ina godewa Allah a kan komai."
"Ziyarata ba ta siyasa ba ce, amma domin in yi ta’aziyya da jajantawa masu jinya, sannan in girmama shugabannin gargajiya da iyayenmu,”

- Farouk Lawan

Lawan ya bayyana cewa tsayayyar akidar siyasa ta tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ita ce ke tabbatar da matsayinsa a yanzu.

Farouk Lawan ya magantu kan siyasarsa

Daga bisani kuma ya ce:

“A yanzu, ina cikin ‘yancin siyasa, ba na cikin kowanne bangare.”

- Farouk Lawan

A bangarensa, hakimin Bagwai, Alhaji Nura Shehu Ahmad ya bayyana zaman gidan yari da Lawan ya yi a matsayin “albarka a boye” ga shi da mabiyansa.

Kara karanta wannan

Halin da ake ciki a Kano bayan hana Sarki Sanusi II fita, an janye jami'an tsaro

Hon. Farouk Lawan ya shaki iskar yanci

Kun ji cewa tsohon dan Majalisar Tarayya a jihar Kano, Farouk Lawan ya samu yanci bayan kama shi da cin hanci da rashawa.

An zargin tsohon dan Majalisar da karbar cin hanci na makudan kudi har $3m a hannun dan kasuwa, Femi Otedola.

Wannan na zuwa ne bayan daure tsohon dan Majalisar har na tsawon shekaru biyar a gidan gyaran hali a Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.