Atiku, Ndume da Wasu Gogaggun Yan Siyasa da Ruka Riƙe Wuta wajen Sukar Tinubu

Atiku, Ndume da Wasu Gogaggun Yan Siyasa da Ruka Riƙe Wuta wajen Sukar Tinubu

  • Shugaban Najeriya, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu yana shan suka daga Kudu da Arewacin Najeriya kan wasu tsare tsarensa
  • Sanata Ali Ndume, Atiku Abubakar da Olusegun Obasanjo na cikin gogaggun yan siyasa a Najeriya da suka matsawa Tinubu lamba
  • A wannan rahoton, mun tattaro muku jerin manyan yan siyasa da irin maganganun da suka yi a kan gwamnatin Bola Tinubu

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Tun da shugaban kasa Bola Tinubu ya hawu mulki ya fara shan suka daga yan siyasa a APC da jam'iyyun adawa.

A mafi yawan lokuta, yan Najeriya na sukar shugaban kasar ne saboda tsare tsaren tattalin arzikin da ya kawo.

Ndume
Yan siyasa da suka saka Tinubu a gaba a Najeriya. Hoto: Bayo Onanuga|Ali Muhammad Ndume
Source: Facebook

A wannan rahoton, mun tattaro muku wasu daga cikin yan siyasa da suka ragargaji gwamnatin Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya fadi abin da ya kamata Najeriya ta koya wajen Faransa

1. Olusegun Obasanjo

Tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo na cikin waɗanda suka matsa lamba ga shugaba Tinubu.

A wurare da dama Olusegun Obasanjo ya sha caccakar Bola Tinubu yana nuna gazawar gwamnatinsa.

Emilokan: Abubuwa sun lalace inji Obasanjo

A wani taro a kasar Amurka, Olusegun Obasanjo ya yi martani mai zafi ga gwamnati inda ya ce lamura sun lalace a mulkin Tinubu, Emilokan.

Obasanjo ya ce duk wani mai hankali da zai fadi gaskiya zai tabbatar da cewa Najeriya ba ta tafiya daidai a mulkin Bola Tinubu.

Tinubu ya yi martani ga Obasanjo

Fadar shugaban kasa ta yi martani ga Obasanjo inda ta ce bai kamata ya yi magana a kan lalacewar Najeriya ba.

Gwamnatin tarayya ta ce Bola Tinubu na gyara kurakuran da Obasanjo ya yi ne a lokacin mulkinsa.

2. Atiku Abubakar

Atiku Abubakar ya kasance babban abokin hamayyar Tinubu a zaben 2023 kuma yana cikin masu matsin lamba ga shugaban kasar.

Kara karanta wannan

Majalisar Dattawa ta tafka muhawara, kudirin harajin Tinubu ya tsallake karatu na 2

Haka zalika fadar shugaban kasa tana mayar da martani ga Atiku a mafi yawan lokuta idan ya ragargaji Tinubu.

Atiku ya kira Tinubu da T Pain

Cikin kalamai masu zafi da Atiku Abubakar ya yi ga Bola Tinubu, akwai kiran shi da T-Pain da ya yi.

The Cable ta wallafa cewa Atiku Abubakar ya ce saboda hali irin na T-Pain, yan kasa na fama da wahala amma kullum yana tafiye tafiye.

Magana kan ciwo bashin Tinubu

A makon da ya wuce gwamnatin Bola Tinubu ta fara maganar ciwo bashin Naira 1.7 tiriliyan domin wasu ayyuka.

Atiku Abubakar ya ragargaji gwamnatin Tinubu kan maganar inda ya ce babu amfanin harajin da ya ce yana tarawa idan zai cigaba da ciwo bashi.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya wallafa a Facebook cewa da alamar akwai abin da Bola Tinubu ke boyewa yan Najeriya kan tattalin kasar.

3. Rabi'u Kwankwaso

Sanata Rabi'u Kwankwaso na cikin manyan yan jam'iyyar adawa da suka caccaki gwamnatin Bola Tinubu.

Sanata Rabi'u Kwankwaso ya yi martani mai zafi a kan kudirin haraji da ake shirin kawowa Najeriya.

Kara karanta wannan

Wasu gwamnonin Arewa sun bi Tinubu Faransa, an fadi abin da za su tattauna

Kwankwaso ya yi zargin cewa kudirin haraji da Bola Tinubu ke shirin kawowa kamar alama cewa da ke nuna ana son bautar da yankunan Arewa daga Legas.

4. Sanata Ali Ndume

Duk da cewa yana jam'iyyar APC, Sanata Ali Ndume ya shahara da caccakan tsare tsaren gwamnatin Bola Tinubu.

Ali Ndume ya kasance daga cikin Sanatoci da suka dade a majalisar dattawa wanda wasu ke ganin gogewarsa na cikin abin da ke ba shi kwarin gwiwar sukar gwamnati.

Magana kan rage farashin abinci

Sanata Ali Ndume ya yi zazzafan caccaka ga gwamnatin Bola Tinubu a kan tsadar rayuwa da ake a Najeriya.

Ali Ndume ya ce tsare tsaren gwamnati sun jefa al'umma a wahala saboda haka akwai buƙatar a rage farashin abinci.

Punch ta wallafa cewa Sanatan ya ce masu ba shugaban kasa shawara na kara dulmiya shi daji a kan halin da ake ciki

A dakatar da Ali Ndume a majalisa

Biyo bayan maganganun da Ali Ndume ya yi, an dakatar da shi daga matsayin mai tsawatarwa a majalisa.

Sai dai daga baya, APC ta masa afuwa bayan ya gana da shugaban jam'iyya na kasa, Abdullahi Ganduje kuma an yi yunkurin mayar da shi kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya dura a ƙasar Faransa, ya fara muhimmin aikin da ya kai shi

Maganar kudirin harajin Tinubu

Sanata Ali Ndume ya bayyana ƙarara cewa zai yi adawa da kudirin harajin Bola Tinubu a majalisa.

Ndume ya ce kudirin harajin yazo a lokacin da yan Najeriya suke fama da wahalhalun rayuwa kuma bai kamata a tabbatar da shi ba.

A ranar 28 ga Nuwamba, Legit ta ruwaito cewa an gwabza tsakanin Ali Ndume da Barau Jibrin a majalisa kan kudirin harajin.

Obi ya ragargaji Tinubu kan lantarki

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon dan takarar shugaban kasa, Peter Obi ya caccaki gwamnatin Bola Ahmed Tinubu kan rashin wutar Arewa.

Peter Obi ya taya yan Arewa bakin cikin duhu da su ka taba shiga na tsawon kwanaki wanda ya jefa jama’a a cikin matsi da karayar tattali.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng