Yan Adawa Sun Fara Wani Shirin Ture Tinubu a Zaɓen 2027
- Yan jam'iyyar Labour sun yi wani taro na musamman domin fara shirin kifar da gwamnatin APC a zaɓen shekarar 2027
- Shugaban tattaro jama'a na jam'iyyar LP, Marcel Ngogbehi ya ce ba za su yi kasa a gwiwa ba har sai sun shiga Aso Rock Villa a 2027
- Marcel Ngogbehi ya kuma bayyana muhimman abubuwan da za su mayar da hankali a kai idan suka samu nasara
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - An yi taron matasan jam'iyyar LP a Abuja domin shirin tunkarar zaben shugaban kasa na shekarar 2027.
A yayin taron, an yi kira ga matasan jam'iyyar da su cigaba da hada kan yan Najeriya domin kafa gwamnati a 2027.
Jaridar Vanguard ta wallafa cewa LP ta ce bangarorin ilimi da tsaro za su samu kulawa idan aka zabe ta a 2027.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
LP ga fara shirin kwace mulki a 2027
Tribune ta walafa cewa Jam'iyyar Labour ta shirya wani taron matasa na kasa domin fara shirin siyasar 2027 mai zuwa.
Mai jagorantar hada kan jama'a a jam'iyyar, Marcel Ngogbehi ya ce za su mayar da hankali a kan neman goyon bayan yan ƙasa a yanzu.
Marcel Ngogbehi ya ce hada kan al'umma na cikin abubuwan da za su ba jam'iyyar hadin kai da karɓuwa a sassan Najeriya.
"Mun shirya wannan taron ne domin neman yadda za mu hada kai mu samar da mafita ga matsalolin Najeriya.
Ina kira a gare ku da ku kulla alaka da mutane, ku sanar da su manufar jam'iyyar mu. Idan muka hada kai za mu iya kawo sauyi.
Ba za mu yi kasa a gwiwa ba har sai mun tabbatar da shugaban kasa a karkashin LP ya shiga Aso Villa."
- Marcel Ngogbehi
Jam'iyyar LP ta ce za ta mayar da hankali kan matsalolin hauhawar farashi, rashin tsaro, matsalar lantarki, ilimi da tattalin arziki.
ACF ta yi magana kan zaben 2027
A wani rahoton, mun ruwaito muku cewa kungiyar dattawa ta ACF ta ce ba za ta zabi kowa ba a 2027 sai wanda ya fito daga Arewa.
An ruwaito cewa Kungiyar dattawan Arewa ta yi magana ne yayin wani taro da ta gudanar a jihar Kaduna a ranar Laraba.
Asali: Legit.ng