'Ka Yi Koyi da El Rufai': Hadimin Buhari Ya Fadi Yadda Abba Kabir Zai Gyara Kano
- Hadimin tsohon shugaban kasa, Bashir Ahmad ya ba gwamnatin Kano shawara kan yadda za ta kawo sauyi a cikin birni
- Mai ba Muhammadu Buhari shawara ya roki Abba Kabir Yusuf ya yi koyi da tsarin tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai
- Bashir Ahmad ya shawarci Abba Kabir ya samar da birane guda biyu a jihar domin rage cunkoso da ke addabar birnin Kano
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - Hadimin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya shawarci Gwamna Abba Kabir kan inganta Kano.
Bashir Ahmad ya bukaci Abba Kabir ya yi koyi da salon tsarin tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai kan bunƙasa birni.
Bashir Ahmad ya ba gwamna Abba shawara
Bashir ya bayyana haka a shafinsa na X a yau Laraba 13 ga watan Nuwambar 2024 inda ya bukaci daukar matakin rage cunkoso a birnin Kano.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsohon hadimin Buhari ya koka kan yadda birnin Kano ke fama da cunkoso da ya cancanci a dauki mataki.
Matashin 'dan siyasar ya ce ya kamata a yi koyi da tsarin ɗa tsohon gwamna, Nasir El-Rufai ya yi a Kaduna
Bashir ya bukaci Abba ya yi koyi da El-Rufai
"Ya kai mai girma gwamna, Abba Kabir Yusuf, ya kamata mu sauya tsarin birnin Kano kamar yadda Kaduna ta yi karkashin mulkin Nasir El-Rufai."
"Ya kamata mu samu akalla birane guda biyu bayan birnin Kano da muke da shi a jihar."
"Misali, a sami birnin Gaya da Danbatta saboda rage cunkoso a Kano domin samun cigaba mai ɗorewa, Allah ya ba da iko."
- Bashir Ahmad
Bashir Ahmad ya yabawa Audu Bako a Kano
Kun ji cewa tsohon hadimin Muhammadu Buhari ya bayyana gwamnan da ya yi fice a jihar Kano wurin kawo ayyukan cigaba.
Bashir Ahmad ya tsallake tsofaffin gwamnoni kamar su Sanata Rabiu Kwankwaso da Abdullahi Umar Ganduje da suka yi mulki.
Bashir ya ce Audu Bako ya yi fice a cikin sauran gwamnoni inda ya ce shi ne ya samar da duk wasu manyan ayyuka a jihar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng