Jaruma Ta 'Koma' Kwankwasiyya bayan Haduwa da Barau da Sunan Barin NNPP
- Ba da dadewa ba aka ga Asma’u Abdullahi Wakili ta shiga cikin jama’an da ke zuwa gidan Sanata Barau Jibrin
- Jarumar ta Kannywood ta fadawa duniya cewa ta rabu da darikar Kwankwasiyya da NNPP mai ci a jihar Kano
- Ana zargin ‘Yar Tik Tok din ta cigaba da bin tafarkin da ta ke kai, ta yi watsi da batun shiga jam’iyyar APC
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Kano - Asma’u Abdullahi Wakili wanda aka ji labarin ta sauya-sheka daga NNPP mai mulkin Kano zuwa jam’iyyar APC.
A wancan lokaci an ji Asma’u Abdullahi Wakili ta yi zama da mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau I. Jibrin.
Haduwar Sanata Barau Jibrin da Asmee
Ba a dade ba sai ga rahoto a tashar Freedom cewa ana zargin an ga ‘yar wasar kwaikwayon ta sake koma gidan jiya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Duk da ta shaidawa duniya cewa ta yi watsi da tafiyar NNPP, sai ga Asmee Wakili ta na jin wakar Kwankwasiyya a Tik Tok.
Karyar sauya sheka tsakanin NNPP da APC
Tun kafin yanzu mabiya darikar Kwankwasiyya ta soki yadda ‘ya ‘yanta su ke ziyartar Sanata Barau Jibrin a birnin Abuja.
Shugabannin NNPP sun ja hankalin sanatan ya yi hankali da masu yaudararsa da sunan cewa sun sauya sheka zuwa APC.
Ana tsoron cewa ‘yar wasa kuma mawakiyar ta yaudari mataimakin shugaban majalisar ne ko kuma akalla ta canza shawara.
Ba wannan ne karon farko da ‘yan jam'iyyar NNPP su ka ziyarci jagororin APC, daga baya kuma suka koma gidan jar tagiya ba.
Asmee ta na rawa bayan ganawa da Barau
A bidiyon da wani Ibrahim Adam ya wallafa a Facebook, an ga jarumar ta na sauraron wakar Dauda Kahutu Rarara a Tik Tok.
‘Yar wasar kwaikwayon ta tiki rawa da ta ke jin wannan waka ta ‘Ga shi Jamila ta yi bari’.
Rahotanni sun ce jarumar ta na cikin yaran Sunusi Oscar wanda gwamna Abba Kabir Yusuf ya nada cikin hadimansa a 2023.
A karshen watan Oktoban 2024 aka ji Oscar ya sauka daga kujerar da yake kai na mai taimakawa gwamna kan sha’anin Kannywood.
Kujerar da ta gagara barin jihar Kano
Wani rahoto na musamman ya nuna an yi shekaru ana samun mai ba shugaban kasa shawara kan sha’anin majalisa daga jihar Kano.
Mai girma Bola Tinubu ya dauko Sanata Bashir Lado a matsayin mai taimaka masa kan batun sha'anin Sanatoci a majalisar dattawa.
Muhammadu Buhari ya dauko Kawu Sumaila a 2015, har yau kujerar ba ta bar Kano ba.
Asali: Legit.ng