Ba Kwankwaso ko Ganduje ba: Hadimin Buhari Ya Fadi Tsohon Gwamnan Kano da Ya Yi Fice
- Tsohon hadimin Muhammadu Buhari ya bayyana gwamnan da ya yi fice a jihar Kano wurin kawo ayyukan cigaba
- Bashir Ahmad ya tsallake tsofaffin gwamnoni kamar su Sanata Rabiu Kwankwaso da Abdullahi Umar Ganduje
- Bashir ya ce Audu Bako ya yi fice a cikin sauran gwamnoni inda ya ce shi ne ya samar da duk wasu manyan ayyuka a jihar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - Hadimin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari a bangaren sadarwa, Bashir Ahmad ya yi magana kan cigaban jihar Kano.
Bashir ya ce ba a taba gwamna a Kano kamar Audu Bako ba wurin kawo ayyukan cigaba a fadin jihar a mulkinsa.
Bashir ya fadi alherin Audu Bako a Kano
Bashir Ahmad ya bayyana haka ne a jiya Juma'a 8 ga watan Nuwambar 2024 a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsohon hadimin Buhari ya ce duk wasu manyan ayyukan alheri da jihar ke mora sanadin tsohon gwamna, Audu Bako ne.
A cikin bayanansa, matashin ya kawar da kai wurin gudunmawar da Rabiu Kwankwaso da Abdullahi Ganduje suka bayar a jihar.
'Ayyukan cigaba da Audu Bako ya yi' - Bashir
"A tarihin jihar Kano, tsohon gwamna Audo Bako ya zama daban daga cikin takwarorinsa wurin gudanar da manyan ayyuka."
"Mafi yawan abubuwam more rayuwa da ake mora a yanzu kamar su sakatariyar jiha da asibitoci da hanyoyi da makarantu da otel otel sanadin Audu Bako ne."
"Sai dai abin takaici, gwamnonin da suka biyo bayansa sun fifita siyasarsu fiye da cigaban jihar."
- Bashir Ahmad
Abba Kabir ya shirya yin garambawul
A baya, kun ji cewa Gwamna Abba Kabir na jihar Kano Yusuf ya yi magana kan shirin yin garambawul a gwamnatinsa nan ba da jimawa ba.
Gwamna Abba Kabir ya bayyana haka ne bayan karbar rahoto na musamman kan kula da ayyukan kwamishinoni a jihar bayan shafe fiye da shekara daya a mulki.
Wannan na zuwa ne yayin da ake zargin rigima tsakanin Abba da mai gidansa, Sanata Rabi'u Kwankwaso wanda ya musanta a lokuta da dama.
Asali: Legit.ng