APC ta Koka kan Zafafan Kalaman da Atiku Ya yi ga Gwamnatin Tinubu

APC ta Koka kan Zafafan Kalaman da Atiku Ya yi ga Gwamnatin Tinubu

  • Jam'iyyar APC mai mulki ta yi martani kan yadda tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ke cigaba da sukan gwamnatin Bola Tinubu
  • APC ta ce bai kamata a matsayinsa na tsohon mataimakin shugaban kasa ya rika sukan gwamnati a kai a kai ba maimakon zamowa dattijon ƙasa
  • Gwamnatin APC ta dauki zafi kan wasu bayanan da Atiku Abubakar ya yi na cewa tsare tsaren Bola Tinubu ne suka jefa al'umma a wahalar rayuwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - An kara samun musayar yawu tsakanin Atiku Abubakar da gwamnatin Bola Tinubu kan yadda za a samar da mafita ga Najeriya.

Jam'iyyar APC mai mulki ta ce Atiku Abubakar ya cika surutu da sukan gwamnatin Bola Tinubu duk da cewa ba haka ya kamata ya yi ba.

Kara karanta wannan

Matasa sun fusata, an mika bukata kan yara da gwamnatin Tinubu ta kai kotu

Atiku
APC ta yi martani da Atiku. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu|Atiku Abubakar
Asali: Getty Images

Rahoton jaridar Vanguard ya nuna cewa APC ta ce shawarar da Atiku ke ba Bola Tinubu kan samar da mafita ba mai ɓullewa ba ce.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Maganar Atiku a kan gwamnatin Bola Tinubu

Atiku Abubakar ya ce duk wahalar rayuwa da aka shiga a Najeriya a sanadiyyar tsare tsaren Bola Ahmed Tinubu ne.

A karkashin haka Atiku ya fadawa Tinubu hanyoyin warware matsalolin kasa amma fadar shugaban kasa ta yi watsi da su.

A karkashin haka Atiku ya kara wasu bayanai bayan gwamnatin tarayya ta shirya taron addu'a a ƙasa wanda hakan ya saka APC yin martani.

Martanin APC ga Atiku Abubakar

APC ta ce martanin da Atiku Abubakar ke yi ga gwamnati ya wuce gona da iri kuma bai kamata ya rika haka ba.

Jam'iyyar ta ce yan Najeriya na bukatar Atiku Abubakar ya zamo dattijon ƙasa maimakon sukan gwamnatin a kai a kai.

Kara karanta wannan

Gwamnati ta yi martani ga Atiku, ta fadi abin da zai faru idan da PDP ke mulki

APC ta ce dole a samu tashin farashin kaya

Tribune ta wallafa cewa APC ta ce maganar tashin farashi da Atiku ke surutu a kai, shi ma ya san dole a samu haka saboda cire tallafin man fetur da aka yi.

Jam'iyyar ta kara da cewa Bola Tinubu zai cigaba da ɗaukar tsauraran matakai da za su kai Najeriya ga tudun tsira a nan gaba.

2027: An bukaci Atiku ya yi takara

A wani rahoton, kun ji cewa wani jigo a PDP, Glintstone Akinniyi ya yi bayanin yadda Atiku Abubakar zai iya lashe tikitin takarar shugaban ƙasa a 2027.

Akinniyi ya ce idan Atiku na son takara ya zama tilas ya fito ya nema, inda ya ƙara da cewa jam'iyyu ba su ba mutum takara sai ya nema.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng