“Babu Abin da Arewa Za Su Yi wa Tinubu”: Aisha Yesufu Kan Tasirinsu a 2027
- Aisha Yesufu ta caccaki yan Arewa kan zaben 2027, ta ce babu abin da yan yankin za su iya yi domin samar da shugaban kasa
- Yesufu ta ce yan Arewa ba za su iya ba Tinubu yawan kuri'un da zai yi nasara ba sai dai wanda zai yi magudi
- Hakan ya biyo bayan halin da ake ciki a kasa inda wasu yan Arewa ke cewa ba za su goyi bayan Tinubu a 2027 ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - 'Yar gwagwarmaya, Aisha Yesufu ta yi magana kan zaben 2027 na shugaban kasa, Bola Tinubu.
Yesufu ta yi magana ne kan yadda yan Arewacin kasar ke bugan kirji kan tasirinsu a zaben shugaban kasa a Najeriya.
2027: Aisha Yesufu ta magantu kan zaben Tinubu
Yar gwagwarmayar ta bayyana haka ne a shafinta na X a yau Alhamis 31 ga watan Oktoban 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yesufu ta ce babu wani tasiri da Arewa ke da shi wurin hana Tinubu ko shugaban kasa cin zabe.
Ta ce Arewa kawai ta ba da kuri'u ne domin samun damar yin magudi a zaben da ya gabata.
"Yan Arewa ba za su iya ba Tinubu yawan kuri'u da zai ci zabe ba, sun ba shi yawan kuri'u ne kawai domin yin magudi."
- Aisha Yesufu
Aisha Yesufu ta magantu kan zaben Buhari
Yar gwagwarmayar ta bayyana haka ne bayan yada wallafa da ya ta yi a ranar 5 ga watan Yulin 2022.
A cikin wallafar, ta ce idan har Arewa suna da karfin mayar da wani shugaban kasa, da sun ba Buhari mulki a zaben shekarar 2003.
"Idan yan Arewa suna da karfin ikon ba da mulkin shugaban kasa, da Buhari ya ci zaben shekarar 2003 da aka yi."
- Aisha Yesufu
Bashir Ahmad ya soki Yesufu kan fim
Kun ji cewa hadimin, tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari a bangaren sadarwa, Bashir Ahmad ya soki Aisha Yesufu bayan ta caccaki Abba Kabir.
Aisha ta caccaki gwamna bayan haramta fina-finan 'yan daudu yayin da ta ke martani kan fitaccen dan daudu, Idris Bobrisky.
Bashir ya nuna goyon bayansa kan matakin da Gwamna Abba Kabir ya dauka inda ya ce su na goyon bayan dakile matsalar a Kano.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng