Sanatocin Arewa da Suka Fi Kowa Gabatar da Kudiri a Majalisar Tarayya cikin Shekara 1

Sanatocin Arewa da Suka Fi Kowa Gabatar da Kudiri a Majalisar Tarayya cikin Shekara 1

Yan Majalisar Tarayya da dama na kokarin gabatar kudurori domin kawo sauyi ga wadanda suke wakilta ko cigaban ƙasa baki daya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Sai dai akwai wasu yan Majalisar Dattawa da ba su tabuka komai ba wurin gabatar da kudiri a Majalisar.

Sanatocin Arewa da suka fi gabatar da kudiri a Majalisar Tarayya
Jerin sanatoci daga Arewacin Najeriya da suka fi gabatar da kudiri a Majalisa. Hoto: Abubakar Sadiq Ahmed, Barau I Jibrin.
Asali: Facebook

Tun bayan dawowa Majalisa ta 10, an samu akalla sanatoci 14 da suka fi kowa gabatar da kudiri daga Mayun 2023 zuwa Mayun 2024, cewar rahoton StatiSense.

Sanatocin da suka fi kudirori a majalisa

Legit Hausa ta binciko muku sanatocin Arewa da suka fi kowa gabatar da yawan kudirori.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

'Yan Najeriya su shirya: Majalisa ta ba CBN sabon umarni na janye tsofaffin Naira

1. Sanata Tahir Monguno - Borno ta Arewa

Tahir Monguno da ke wakiltar mazabar Borno ta Arewa yana daga cikin sanatoci da ke ba da gudunmawa sosai.

Sanata Monguno a cikin shekara daya kacal a Majalisar ya gabatar da kudiri guda 23 wanda shi ne yafi kowa.

Bangaren da sanatan ya fi ba da karfi su ne fannin rashin tsaro da harkokin ilimi da kuma ayyukan raya kasa.

Daga cikin kudurorin da Monguno ya gabatar a 2023 akwai kudiri kan rijistar kungiyar masu siyar da abinci da ya tsallake karatu na farko.

2. Sanata Barau Jibrin - Kano ta Arewa

Barau Jibrin daga jihar Kano ya kasance na biyu a jerin wadanda suka fi gabatar da kudiri a Majalisar.

Sanata Barau da ke wakiltar Kano ta Arewa ya gabatar da kudurori akalla guda 22 daga Mayun 2023 zuwa Mayun 2024.

A watan Yuli da Agustan 2023 Sanata Barau Jibrin ya gabatar da kudurori kamar yadda Majalisar ta tabbatar.

Kara karanta wannan

NDLEA: Majalisa ta dauki mataki kan zargin kama kwayoyi a gidan sanata

Sannan a watan Oktoban 2023 ya gabatar da kudurori da iska hada da Kwalejin Gwamnatin Tarayyar a Kano da da Jami'ar Tarayya a Bichi.

Sannan akwai na abubuwa masu fashewa da wanda ya shafi laifuffukan yanar gizo da kudiri game da Kwalejin ilimi a Kano.

3. Sanata Aliyu Wadada - Nasarawa ta Yamma

Sanata Aliyu Wadada da ke wakiltar Nasarawa ta Yamma shi ne yazo na uku a jerin wadanda suka fi gabatar da kudiri.

Wadada ya gabatar da kudurori akalla guda 10 a cikin shekara daya da aka yi a Majalisar ta 10.

Daga cikin kudurori 15 da Sanatoci daga Nasarawa suka gabatar, Sanata Wadada ne ya gabatar da guda 10.

Kamar yadda OrderPaper ta ruwaito, kaso 90 na duka kudurorin da Wadada ya gabatar suna jiran karatu na biyu.

4. Sanata Sani Musa - Niger ta Gabas

Sanata Sani Musa ya kasance na hudu a jerin sanatocin Arewa da suka fi kowa gabatar da kudiri a Majalisar cikin shekara daya.

Kara karanta wannan

Barayi sun tasa Abuja a gaba, majalisa ta gayyato Ministan Tinubu da DSS

Sani Musa shi ma ya gabatar da kudiri guda 10 kamar Sanata Wadada daga jihar Nasarawa a Arewacin Najeriya.

Daga cikin kudirin da Sanata Musa ya gabatar a watan Yulin 2023 akwai bangaren inganta fasahar zamani da kirkire-kirkire.

Sannan a watan Satumbar 2023 akwai kudirin kare manyan ayyukan gwamnati da na hukumar raya yankin Arewa ta Tsakiya, cewar rahoton Majalisar.

Sauran sanatocin Kudu masu kokari a majalisa

Michael Bamidele - Ekiti ta Tsakiya - 17

Asuquo Ekpenyong - Cross River ta Kudu - 13

Daniel Oluwagbenga - Ogun ta Gabas - 13

Orji Kalu - Abia ta Arewa - 12

Mukhail Abiru - Lagos ta Gabas - 12

Olamilekan Solomon - Ogun ta Yamma - 12

Banigo Harry - Rivers ta Yamma - 11

Sanatocin Arewa da ba su gabatar da kudiri ba

Mun ba ku labarin cewa akwai wasu tsofaffin gwamnoni da ke Majalisa da kuma sanatoci da ba su gabatar da kudiri ko daya ba a watanni 10.

Kara karanta wannan

Ana rade radin rigimar Abba da Kwankwaso, an kori yan jaridu daga gidan gwamnati

Akalla akwai tsoffin gwamnonin 13 a Majalisar wanda hudu daga cikinsu ba su yi wani katabus ba tun bayan shigowarsu Majalisar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.