Kwankwasiyya Ta Yi Rashi, 'Yar Uwar Sakataren Gwamnatin Kano Ta Koma Jam'iyyar APC
- Jam'iyyar NNPP ta yi babban rashi a jihar Kano yayin da 'yar uwar sakataren gwamnatin jihar Kano (SGG), Dakta Baffa Bichi ta koma APC
- Hajiya Lami Bichi tare da tawagarta sun hakura da tafiyar Kwankwasiyya inda suka gana da Sanata Barau Jibrin domin su sauya-sheka
- Jagorar mata a Kano, ta ce nan gaba kadan za ta jawo dan uwanta, Baffa Bichi zuwa jam'iyyar APC 'domin kawo ci gaba a Kano da kasa'
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Hajiya Lami, wata kanwar sakataren gwamnatin jihar Kano (SGG), Dakta Baffa Bichi ta fice daga jam’iyyar NNPP zuwa APC mai mulki a kasa.
Mai fafutukar mata a Kano, Hajiya Lami ta bayyana ficewa daga NNPP a gidan mataimakin shugaban majalisar dattawa Sanata Barau I Jibrin da ke Abuja.
Hajiya Lami ta kuma bayyana cewa nan ba da jimawa ba za ta jawo yayan nata, Dakta Baffa Bichi zuwa jam'iyyar APC, inji rahoton Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Alakar siyasa tsakanin Barau da Baffa
Dakta Baffa Bichi ya taba rike mukamin babban sakatare na asusun TetFund tsakanin 2016 zuwa 2019 a lokacin gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari.
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ne ya nada shi a matsayin sakataren gwamnatin jihar a ranar 30 ga Mayu, 2023.
A watan Fabrairun 2023 Barau ya doke Baffa Bichi, dan takarar kujerar sanatan Kano ta Arewa a karkashin Jam’iyyar NNPP.
Shi kadai ne sanatan da APC ta samu daga jihar Kano. Bayan nan sai ya zama mataimakin shugaban majalisar dattawa.
Sanata Barau wanda ya yi takara karkashin APC ya samu kuri’u 234,652 inda shi kuma Dakta Baffa ya samu kuri’u 177,014.
Kanwar Baffa ta sauya sheka zuwa APC
A yayin da take sanar da sauya shekarta daga tafiyar Kwankwasiyya zuwa APC, jaridar Leadership ta rahoto Hajiya Lami ta ce:
"A yau tare da abokaina na harkar siyasa a fadin Kano, mun fice daga NNPP zuwa APC, za mu hada karfi da karfe domin tunkarar kalubalen da jiharmu da kasarmu ke fuskanta.
Zan jawo dan uwana Baffa Bichi zuwa APC na ba da jimawa ba."
Da yake mayar da martani, Sanata Barau ya yi maraba da Hajiya Lami da tawagarta zuwa APC, inda ya ba su tabbacin cewa jam’iyyar ba za ta ba su kunya ba.
Daruruwan 'yan NNPP sun koma APC
A wani labarin, mun ruwaito cewa mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin ya karbi daruruwan 'yan jam'iyyar NNPP a Kano da suka koma APC.
Sanata Barau ya ce wadanda suka sauya shekar sun same shi a ofishinsa da ke a majalisar tarayya karkashin kungiyoyi biyar domin sanar da ficewarsu daga tafiyar Kwankwasiyya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng