Ganduje: Dakta Baffa Bichi na APC ya ziyarci Abba Gida-gida har gida
Dakta Baffa Bichi, tsohon babban sakataren hukumar asusun manyan makarantun na kasa (TETFUND), ya kai ziyarar ban girma ga Abba Kabir Yusuf, dan tgakarar gwamnan jihar Kano a karkashin inuwar jam’iyyar PDP, domin nuna baya gare shi a bayyane.
A wani faifan bidiyo da Salihu Tanko Yakasai, mai taimakawa gwamnan jihar Kano a bangaren sadarwar zamani, ya fitar a shafinsa na Tuwita a yau, Litinin, an ga Dakta Bichi tare da Abba sun cikin farinciki da walwala sun a gaisawa da jama’a kafin daga bisani su shiga wani daki.
Yakasai ya bayyana cewar Dakta Bichi ya ziyarci Abba ne domin nuna goyon baya gare shi a bayyane, a kokarinsa na daukar fansa a kan Ganduje da jam’iyyar APC saboda an cire shi daga mukaminsa.
A watan Janairu ne aka cire Dakta Bichi daga mukaminsa na babban sakataren TETFUND bisa zarginsa da saba ka’idoji wajen gudanar da aikinsa.
Sai dai, Dakta Bichi ya musanta wannan zargi tare da bayyana cewar an cire shi daga mukamin nasa ne saboda ya ki yarda a yi amfani da ofishinsa a kwashi wasu makudan kudi domin taimakon wata kungiyar addini.
Dakta Bichi ya kirkiri kungiyar ‘one 2 tell 10’ da ta yi wa shugaban kasa Muhammadu Buhari yakin neman zabe a jihohin arewa 19.
An sha yin rade-radin cewar dangantaka tsakanin Dakta Bichi da gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ta dade da yin tsami.
Wasu na alakanta rashin jituwar dake tsakaninsu da dalilai na siyasa da kuma nuna iko da isa a al’amuran tafiyar da yakin shugaban kasa a jihar Kano.
DUBA WANNAN: Badakalar N544m: EFCC ta yiwa tuhumar Babachir kwaskwarima
Ana ganin cewar Dakta Bichi na son yin amfani da damar sake maimaita zabe a wasu mazabun jihar Kano domin daukar fansar raba shi da mukamin sa da yake zargin har da gwamna Ganduje a ciki.
Dakta Bichi bai ce uffan ba a kan faifan bidiyon har ya zuwa lokacin da aka wallafa rahoto.
Kazalika jam’iyyar APC a jihar Kano ba ta ce komai ba a kan bayyanar faifan bidiyon ba.
Kafin bullar wannan faifan bidiyo, babu rahoton cewar Dakta Bichi ya fita daga jam’iyyar APC.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng