'Tinubu Muka Zaba,' Tsohon Gwamnan PDP Ya Tono Yadda Suka Kifar da Atiku a 2023

'Tinubu Muka Zaba,' Tsohon Gwamnan PDP Ya Tono Yadda Suka Kifar da Atiku a 2023

  • Tsohon gwamnan jihar Rivers kuma ministan Abuja, Nyesom Ezonwo Wike ya yi magana kan zaben shugaban kasar da ya wuce
  • Nyesom Ezonwo Wike ya ce bai yi nadama ba a kan yadda ya juya baya ga tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar a 2023
  • Haka zalika ministan ya bayyana yadda suka hada kai wajen kawo gwamna Siminalayi Fubara a jihar Rivers a karkashin PDP

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Tsohon gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike ya bayyana dalilin da ya sanya shi juwa baya ga jam'iyyar PDP a zaben shugaban kasar 2023.

Nyesom Ezonwo Wike ya ce bai yi nadamar goyon bayan shugaba kasa Bola Ahmed Tinubu ba a zaben shekarar 2023.

Kara karanta wannan

Atiku ko Wike? Shugabanni sun bayyana wanda ya haddasa rikicin da ya mamaye PDP

Wike da Atiku
Wike ya fadi dalilin goyon bayan Tinubu a kan Atiku. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu|Nyesom Wike|Atiku Abubakar
Asali: Facebook

Minista Abuja, Nyesom Wike ya yi bayani ne a wata hira da ya yi da Channels Television a yammacin ranar Talata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Nyesom Wike ya fadi dalilin kin goyon bayan Atiku

Tsohon gwamnan Rivers, Nyesom Wike ya ce yana sane yaki zaben Atiku Abubakar a zaben shugaban kasar 2023.

Nyesom Wike ya ce ya ki zaben Atiku Abubakar ne domin kaucewa goyon bayan zalunci da rashin gaskiya da aka yi.

Wike ya goyi bayan PDP a zaben gwamnoni

Vanguard ta wallafa cewa Nyesom Wike ya bayyana cewa duk da kin zaben Atiku Abubakar, ya goyi bayan jam'iyyar PDP a zaben gwamnoni.

Haka zalika ministan Abujan ya tabbatar da cewa goyon bayan da suka ba PDP ya jawo samun kujerun majalisar tarayya a jihar.

Ko Wike zai bar jam'iyyar PDP?

Ministan Abuja ya jaddada cewa har yanzu shi cikakken dan PDP ne duk da kasancewar yana rike da mukamin minista a karkashin shugaban kasar APC.

Kara karanta wannan

Nyesom Wike ya bayyana dalilin barkewar rikici a jihar Rivers

Nyesom Wike ya kuma kara da cewa har yanzu bai yi nadama ba kan goyon bayan APC da ya yi a kan jam'iyyarsa ta PDP a babban zaben 2023.

Wike ya magantu kan rikicin Rivers

A wani rahoton, kun ji cewa ministan babban birnin tarayya Abuja ya taɓo batun rikicin da ke aukuwa a jihar Rivers mai arziƙin man fetur.

An ruwaito cewa Nyesom Wike ya bayyana cewa gwamnan jihar, Siminalayi Fubara ne ke da alhaki kan abubuwan da suke faruwa a jihar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng