Doguwa: 'Dalilin da Ya Sa 'Yan Kwankwasiyya Ke Sauya Sheka zuwa APC a Kano'

Doguwa: 'Dalilin da Ya Sa 'Yan Kwankwasiyya Ke Sauya Sheka zuwa APC a Kano'

  • Shugaban masu rinjaye a majalisar wakilai, Alhassan Ado Doguwa ya ce 'yan NNPP sun dawo daga rakiyar gwamnatin Abba Yusuf
  • Ado Doguwa ya ce gwamnatin jihar Kano karkashin Abba ta gaza ta kowace fuska shi ya sa 'yan Kwankwasiyya ke sulalewa zuwa APC
  • Dan majalisar wakilan ya ce duk wani surutu da Rabiu Musa Kwankwaso zai yi ba zai hana jam'iyyar APC karbar mulkin Kano a 2027 ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Hon. Alhassan Ado Doguwa, ya sake yi wa jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwanwaso shagube kan sulalewar 'yan NNPP zuwa jam'iyyar APC.

Shugaban masu rinjaye na majalisar wakilan, Ado Doguwa ya ce 'yan jam’iyyar NNPP a jihar Kano na sauya sheka zuwa APC saboda sun rasa kwarin gwiwa.

Kara karanta wannan

"An kusa daina ganin jar hula": Jam'iyyar APC ta ƙara rikita NNPP a jihar Kano

Ado Doguwa ya yi magana kan sauya shekar 'yan NNPP zuwa APC a Kano
Kano: Ado Doguwa ya bayyana dalilin da ya sa 'yan NNPP ke sauya sheka zuwa APC. Hoto: @aadoguwa, @KwankwasoRM
Asali: Facebook

Ado Doguwa, dan jam’iyyar APC daga jihar Kano ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya aikewa Premium Times a ranar Juma’a.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jam'iyyar NNPP ita ce mai mulki a Kano, karkashin gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf wanda yake da goyon bayan Rabiu Kwankwaso.

Guguwar sauya sheka a jihar Kano

Wasu ‘ya’yan jam’iyyar ta NNPP wadanda suka hada da masu taimakawa Gwamna Abba Yusuf sun sauya sheka zuwa APC a 'yan kwanakin nan.

A watan Agusta, babban mai ba gwamna shawara kan harkokin kasuwanci Abdulraham Kadamaz ya yi murabus daga gwamnati da jam'iyyar zuwa APC.

A watan Satumba, mai ba wamna shawara na musamman kan harkokin zuba jari Sani Dambo, shi ma ya yi murabus, ya koma jam'iyyar APC.

An samu dandanzon 'yan TikTok da kuma manyan jaruman Kannywood da mawaka da suka hakura da tafiyar Kwankwasiyya suka koma APC.

Kara karanta wannan

Ganduje ya bayyana wanda ya ceci jam’iyyar APC daga asarar Naira biliyan 1.5

Doguwa ya soki Kwankwaso, NNPP

Ado Doguwa, wanda ke wakiltar mazabar Doguwa/Tudun Wada ta Jihar Kano, ya ce ‘ya’yan NNPP na ficewa daga jam’iyyar ne saboda gwamnatin Abba ta gaza.

Ya ce jam’iyyar APC na shirin karbar mulki a jihar a 2027 lokacin da za a gudanar da zaben gwamna mai zuwa.

Dan majalisar ya kuma bukaci ‘yan tafiyar Kwankwasiyya a jihar da su hada karfi da karfe da jam’iyyar APC domin samun kyakkyawan shugabanci.

Ado Doguwa ya ce:

“Gwamnatin NNPP ta riga da ta samu matsala, ta raba gari da mutanen kirki na jihar Kano. Duk wani surutu da Rabiu Kwankwaso zai yi, sai APC ta kwace Kano a zaben 2027.
"Mutane sun riga da sun dawo daga rakiyar gwamnatin NNPP a Kano, sun gaji da salon mulkinsu, sun saba alkawuran da suka dauka, wannan zai ba mu nasara."

"A firgice kake" - Doguwa ga Kwankwaso

Kara karanta wannan

"Har yanzu a firgice ka ke": Doguwa ya mayarwa Kwankwaso martani kan kalamansa

A wani labarin, mun ruwaito cewa shugaban masu rinjaye a majalisar wakilai, Alhassan Ado Doguwa ya soki Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Ado Dgouwa ya ce har yanzu Kwankwaso a figice yake kuma bai gama warkewa daga kayen da ya sha a zaben 2027 don haka ya daina magana a madadin 'yan Arewa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.