Ribas: Gwamna Zai Rantsar da 'Yan Jam'iyyar Adawa da Suka Lashe Zaben Ciyamomi

Ribas: Gwamna Zai Rantsar da 'Yan Jam'iyyar Adawa da Suka Lashe Zaben Ciyamomi

  • A yau Lahadi ne gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara, a zai rantsar da zababbun ciyamomi da kansiloli a zauren majalisar zartarwa
  • Wannan na kunshe a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun sakataren gwamnatin jihar Dr Tammy Danagogo, mai kwanan wata 6 ga Oktoba
  • A cewar sanarwar, ana sa ran sababbin zababbun shugabannin, tare da bako guda daya ga kowane za su hallara da misalin karfe 3:30 na rana

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Ribas - Gwamnatin jihar Ribas za ta rantsar da ciyamomi 23 da ta bayyana a matsayin wadanda suka lashe zaben kananan hukumomin da aka gudanar a ranar Asabar.

Gwamnatin jihar ta kuma tabbatar da cewa an kammala zaben, kuma za ta rantsar da wadanda suka yi nasara a yau.

Kara karanta wannan

Fargabar barkewar ambaliya: Gwamnati ta aika sakon gaggawa ga mazauna jihar Kwara

Gwamnatin Ribas ta sanya lokacin rantsar da sababbin shugabannin kananan hukumomi
Ribas: Fubara zai rantsar da zababbun ciyamomi a yau Lahadi. Hoto: @SimFubaraKSC
Asali: Twitter

Fuba zai rantsar da ciyamomi 23

A wata sanarwa dauke da sa hannun sakataren gwamnatin jihar Dr Tammy Wenike Danagogo, an bayyana cewa za a rantsar da ciyamomin da karfe hudu na yamma, inji Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta ce:

"Gwamnan jihar Ribas, Sir Siminalayi Fubara, zai rantsar zababbun ciyamo da kansiloli a gidan gwamnati da ke Fatakwal a yau Lahadi 6 ga Oktoba, 2024 da karfe 4 na yamma."

Yayin da aka ba kowane shugabannin karamar hukuma da aka zaba damar zuwa da bako daya, an ce za su taru a dakin rantsarwar da karfe 3:30 na rana.

Yadda zaben ciyamomin ya gudana

Idan dai za a iya tunawa, an gudanar da zaben ne a jiya cikin tashe tashen hankula da suka hada da harbin bindiga, tashin bam da kuma zanga zanga.

Wannan ci gaban, wanda tuni aka yi hasashen faruwarsa ya sa mazauna jihar da dama cikin damuwa, musamman sakamakon karancin ‘yan sanda a rumfunan zabe.

Kara karanta wannan

Sauye sauye a majalisar ministoci: Tinubu zai saki sunayen ministocin da zai kora

Jaridar Vanguard ta ranar Lahadi ta lura cewa, mutane sun fito sun kada kuri'unsu ba tare da la’akari da fargabar tashin hankalin da ake fama da ita a kananan hukumomi 23 ba.

APP ta lashe zaben ciyamomin Ribas

Tun da fari, mun ruwaito cewa wata bakuwar jam'iyya da Gwamna Siminalayi Fubara ya tura mutanensa su yi takara a cikinta ta lashe kujerun ciyamomi 22 cikin 23 na Ribas.

Babban jami’in zaben jihar, Mai shari’a Adolphus Enebeli, ya bayyana sakamakon zaben a Fatakwal a daren ranar Asabar inda ya ce 'yan takarar APP ne suka lashe zaben.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.