Hukumar zaɓe ta sanar da sakamakon zaɓen kananan hukumomi 13 na jihar Nasarawa
- Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Nasarawa (NASIEC), Ayuba Wadai, ya sanar da sakamakon zaɓen kananan hukumomi 13 na jihar
- Shugaban NASIEC, ya bayyana cewa jam'iyyar APC mai mulkin jihar ce ta samu nasara a baki ɗaya kujerun ciyamomi 13 da kansiloli 147
- Wadai yace zaɓen ya gudana cikin lumana da kwanciyar hankali, matsala ɗaya aka samu na rashin zuwan kayan zabe da wuri
Nasarawa - Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta lashe baki ɗaya kujerun da aka fafata a zaɓen ƙananan hukumomin jihar Nasarawa da ya gudana ranar Laraba, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar, Ayuba Wandai, shine ya bayyana ne yayin da yake sanar da sakamakon zaɓen ranar Alhamis a Lafia, babban brinin jihar.
Wandai yace jam'iyyar APC ta lashe kujerun ciyaman da na kansiloli a baki ɗaya kananan hukumomi 13 dake faɗin jihar Nasarawa.
A jawabinsa, Wandai yace:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Bisa nauyin da aka ɗora mun a matsayin shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta kuma baturen zaɓe na jihar Nasarawa."
"Ina mai bayyana yan takarar APC a zaɓen ciyaman na kananan hukumomi 13 a matsayin waɗanda suka samu nasara kuma suka zama zaɓaɓɓun ciyamomi."
"Hakanan kuma a zaɓen kansiloli da ya gudana a gundumomi 147, yan takarar jam'iyyar APC ne suka lashe dukkan kujerun."
Jam'iyyu nawa ne suka fafata a zaɓen?
Shugaban hukumar zaɓen ya bayyana cewa jam'iyyun ADC, APC, LP, NNPP, PDP, SDP da kuma ZLP ne suka fafata a zaɓen, kamar yadda Guardian ta ruwaito.
Yace a rahoton da ya samu, an gudanar da zaɓen cikin lumana da kwanciyar hankali a faɗin jihar Nasarawa.
A cewarsa matsalar da aka samu guda ɗaya itace rashin isar kayayyakin zabe zuwa rumfunan zaɓe da wuri.
"Hukumar NASIEC ta gudanar da sahihi kuma ingantaccen zaɓe da yafi kowanne, bisa bin ƙa'idoji da dokokin zaɓe na jihar."
A wani labarin kuma kun ji cewa Tsohon ministan Ayyuka a Najeriya ya bayyana mutumin da ya dace APC ta tsayar ya gaji shugaba Buhari
A hasashen, Adeseye Ogunlewe, ya bayyana cewa jigon APC, Bola Tinubu, shi ne ya fi cancanta ya gaji shugaba Buhari a 2023.
Ogunlewe ya bayyana cewa a ranar Alhamis mai zuwa za'a ƙaddamar da tawagar yaƙin neman zaɓen Tinubu reshen mahaifarsa, jihar Legas.
Asali: Legit.ng