Yadda ta kaya tsakanin APC da ragowar jam’iyyu a zaben kananan hukumomin jihar Nasarawa

Yadda ta kaya tsakanin APC da ragowar jam’iyyu a zaben kananan hukumomin jihar Nasarawa

Hukumar zabe ta jihar Nasarawa (NASIEC) ta bayyana jam’iyyar APC a matsayin wacce ta lashe dukkan kujerun da aka gudanar da zabe a kan su a jihar, ranar Asabar, 26 ga watan Mayu, 2018.

Shugaban hukumar zabe a jihar, Henry Omaku, ya sanar da sakamaon a jiya, Lahadi, a shelkwatar hukumar dake Lafia, babban birnin jihar Nasarawa.

Ya bayyana cewar, jam’iyyu ukun; APC, SDP, da ADP, ne suka shiga zaben neman shugabannin kananan hukumomi 13 dake jihar, yayin da jam’iyyu 21 suka shiga zaben neman kujerun kansiloli 147 dake fadin jihar, wadanda kuma jam’iyyar APC ta lashe dukkan su.

Umar Abubakar, dan takarar jam’iyyar APC a samu nasarar lashe zaben karamar hukumar Awe da kuri’u 56,598, yayin da Samuel Meshi ya samu nasara a karamar hukumar Akwanga da kuri’u 50,149.

Yadda ta kaya tsakanin APC da ragowar jam’iyyu a zaben kananan hukumomin jihar Nasarawa
Masu kada kuri'a

A karamar hukumar Nasarawa Eggon, Idris Danlami, ya samu nasara da kuri’u 79,789, Mohammed Sani ya samu nasarar lashe zabe a karamar hukumar Nasarawa, yayin da a karamar hukumar Obi, Mohammed Iyimoga, ya samu nasara da kuri’u 88,019.

Ragowar wadanda suka samu nasara a zaben sun hada da; Aminu Maifata, a matsayin shugaban karamar hukumar Lafia, Saidu Kazi a matsayin shugaban karamar hukumar Kokona da kuma Adamu Giza, a matsayin shugaban karamar hukumar Keana.

DUBA WANNAN: Komawa ga Allah ne mafita ba zargin shugaba Buhari ba

A karamar hukumar Wamba, Abubakar Abbas ne ya samu nasara da kuri’u 27,108, Rabo Sani , ya samu nasara a karamar hukumar Doma da kuri’u 77,003, Samuel Akala ya samu nasara a karamar hukmar Karu da kuri’u 80,934 sai Abdulrahman Sani day a samunasara a karamar hukumar Keffi da kuri’u 14,817.

Jam’iyyun adawa na PDP da APGA sun kauracewa shiga zaben bisa zargin cewar hukumar NASIEC ba zata yi masu adalci.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel