Abbas: Kakakin Majalisar Wakilai na Fuskantar Matsala a APC kan Nada Hadimai 600

Abbas: Kakakin Majalisar Wakilai na Fuskantar Matsala a APC kan Nada Hadimai 600

  • Wani jagora a APC, Taslim Dan-Wanki ya kalubalanci kakakin majalisar wakilai, Hon. Tajudeen Abbas kan nada hadimai 600 da ya yi
  • Ba nada hadiman ne ya damu jigon APC ba, illa dai ya yi ikirarin cewa Tajudeen ya nada 'yan jam'iyyar adawa a wadannan mukamai
  • Dan-Wanki ya nuna cewa shugaban majalisar ya ci amanar da 'yan APC suka dora masa kuma zai ba jam'iyyar matsala a majalisar wakilai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Nada hadimai 600 da kakakin majalisar wakilai, Hon. Tajudeen Abbas ya yi ya jawo ce-ce-ku-ce a cikin jam'iyyar APC musamman bayan maganar Taslim Dan-Wanki.

Jigon APC, Taslim Dan-Wanki ya caccaki kakakin majalisar kan wadannan nade nade da ya yi inda har ya ke kalubalantar nagartarsa a siyasa.

Kara karanta wannan

Damagum: Jerin gwamnoni 6 da ke goyon bayan a tsige shugaban PDP na kasa

Jigon APC ya yi magana kan hadimai 600 da kakakin majalisar wakilai ya nada
Kakakin majalisar wakilai na fuskantar matsin lamba kan nada hadimai 600. Hoto: @Speaker_Abbas
Asali: Facebook

An soki kakakin majalisa kan nadin hadimai

Jigon na APC ya koka kan matakin da Abbas ya dauka na nada 'yan jam’iyyar adawa ta PDP sama da 600 a matsayin manyan hadimansa, inji rahoton The Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Taslim Dan-Wanki ya ce wannan mataki na kakakin majalisar ya jefa mutane a wasi-wasin jam'iyyar Hon. Tajudeen ya ke yiwa biyayya da kuma inda ya dosa a siyasa.

Dan Wanki, wanda ya kware a fafutukar hada kan jam'iyya ya fitar da sanarwa kan lamarin yana mai cewa nade-naden zai kawo rauni ga APC a majalisar tarayya.

"Zai gurgunta tasirin APC" - Dan-Wanki

Dan wanki ya bayyana cewa:

"Nada 'yan jam'iyyar adawa zuwa manyan mukamai na majalisa zai iya kawo cikas ga yadda APC za ta iya aiwatar da manufofinta ta hanyar majalisar tarayya."

Dan Wanki ya bayyana matakin da kakakin majalisar ya dauka a matsayin ‘cin amana' da magoya bayan APC suka dora masa, wanda hakan zai gurgunta jam’iyyar a majalisar wakilai.

Kara karanta wannan

Edo 2024: Yadda APC ta lashe zabe bayan samun nasara a kananan hukumomi 11

Sai dai bangaren kakakin majalisar ya kare nade naden yana mau cewa an yi ne bisa cancanta da kuma bukatar inganta hadin gwiwa a tsakanin jam’iyyun kasar a majalisar wakilai.

Rt. Hon. Tajudeen Abbas ya nada kakakinsa

A wani labarin, mun ruwaito cewa sabon kakakin majalisar wakilai, Hon. Tajudeen Abbas ya nada Musa Krishi a matsayin mai magana da yawunsa.

Hon. Tajudeen Abbas ya tabbatar da wannan nadin Krishi, dan asalin jihar Nasarawa a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis, 15 ga watan Yunin 2023.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.