Abbas Tajudeen, Sabon Kakakin Majalisar Wakilai Ya Nada Hadimai Biyu

Abbas Tajudeen, Sabon Kakakin Majalisar Wakilai Ya Nada Hadimai Biyu

  • Kakakin majalisar wakilan tarayya, Honorabul Tajudeen Abbas, ya fara naɗa hadiman da zasu taimaka masa a majalisa ta 10
  • Abbas ya naɗa tsohon sakataren watsa labaran Gbajabiamila a matsayin mai ba shi shawara kan yaɗa labarai da midiya
  • Haka nan sabon kakakin ya naɗa Jerry Uhuo a matsayin hadiminsa na fannin tsare-tsare da dabaru

Abuja - Sabon kakakin majalisar wakilan tarayya, Abbas Tajudeen, ya naɗa Musa Krishi a matsayin mai ba shi shawara ta musamman kan yaɗa labarai da midiya.

Jaridar Punch ta rahoto cewa Musa Krishi, shi ne tsohon Sakataren watsa labarai na tsohon shugaban majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila.

Sabon kakakin majalisa, Abbas Tajudeen da Musa.
Abbas Tajudeen, Sabon Kakakin Majalisar Wakilai Ya Nada Hadimai Biyu Hoto: thecable
Asali: UGC

Abbas ya tabbatar da wannan naɗi ne a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis, 15 ga watan Yuni, mai taken, "Naɗin mai ba da shawara kan harkokin yaɗa labarai da midiya."

Kara karanta wannan

Cikakken Jerin Sunaye: Shugaba Tinubu Ya Naɗa Nuhu Ribaɗo da Wasu Mutum 7 a Manyan Muƙamai

Sanarwan ta ce:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Ina mai farin cikin sanar da cewa na naɗa Musa Abdullahi Krishi a matsayin mai ba da shawara kan yaɗa labarai da midiya, naɗin zai fara aiki nan take."

Wanene Musa Krishi sabon mai magana da yawun Abbas?

A cewar sanarwan, Musa Krishi, tsohon ma'aikaci ne a jaridar Daily Trust kuma ya fito ne daga jihar Nasarawa da ke Arewa ta Tsakiya a Najeriya.

Ya kammala karatun Diploma ta gaɓa da Digirin farko a jami'ar Bayero da ke Kano (BUK) inda ya gama da mataki mafi daraja kuma ɗalibin da ya fi kowane hazaƙa a wannan shekara.

"Ya yi aiki a matsayin Sakataren watsa labarai na tsohon kakakin majalisar tarayya da ya gabata, Femi Gabajabiamila, daga 2019 zuwa 2023."
"Muna fatan sabon mai magana da yawun kakakin zai amfani da gogewar da ya samu tsawon shekaru wajen cimma kudirin majalisa ta 10," inji sanarwan.

Kara karanta wannan

Majalisar Dokokin Kano Ta Fara Aiki Gadan-Gadan, Ta Amince Abba Gida-Gida Ya Naɗa Hadimai 20

Sabon kakakin ya ƙara wani naɗi na 2

Bugu da ƙari, Tajudeen Abbas, ya naɗa Dakta Jerry Uhuo, a matsayin mai ba da shawara ta musamman kan tsare-tsare da dabaru.

Ya kuma bayyana cewa wannan naɗin zai fara aiki daga yau Alhamis, 15 ga watan Yuni, 2023, kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Shugaba Tinubu Ya Sa Labule da Tsohon Sarkin Kano, Sanusi Lamido a Villa

A wani labarin kuma Shugaban kasa Tinubu ya shiga ganawa da Sarkin Kano na 14, Sanusi Lamido Sanusi, a fadarsa da ke birnin tarayya Abuja.

Haka nan wannan ganawa na zuwa ne mako guda bayan shugaban ƙasa Tinubu ya dakatar da Mista Godwin Emefeliele daga matsayin gwamnan CBN.

Asali: Legit.ng

Online view pixel