PDP ta Gamu da Cikas, Mutum 10,000 cikin Magoya bayan Tsohon Sanata Sun Koma APC

PDP ta Gamu da Cikas, Mutum 10,000 cikin Magoya bayan Tsohon Sanata Sun Koma APC

  • Mutane 10,000 daga cikin magoya bayan tsohon sanatan Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani sun sauya sheka daga PDP zuwa jam'iyyar APC
  • Wadanda suka sauya shekar sun kuma bayyana yakininsu na cewa shi ma tsohon sanatan zai koma APC nan da wasu makonni masu zuwa
  • Sauya shekar dubunnan mutanen dai na zuwa ne kasa da awanni 24 bayan da PDP ta sanar da sababbin shugabanninta na Kaduna

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kaduna - Jam'iyyar PDP ta samu koma baya a jihar Kaduna bayan da magoya bayan Sanata Shehu Sani suka sauya sheka zuwa APC mai mulki.

Mutane 10,000 daga cikin magoya bayan tsohon sanatan suka koma APC a ranar Lahadi kasa da awanni 24 bayan nada shugabannin PDP na Kaduna.

Kara karanta wannan

Zaben Edo: ‘Wakilan APC da PDP na ba masu kada kuri'a cin hancin N10000’

Magoya bayan Sanata Shehu Sani sun fice daga PDP, sun koma APC
Kaduna: Dubunnan magoya bayan Sanata Shehu Sani sun hakura da PDP, sun koma jam'iyyar APC. Hoto: @ShehuSani
Asali: Twitter

Masoyan Sanata Shehu Sani sun koma APC

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa wadanda suka sauya shekar sun fito ne daga kananan hukumomi 23 na jihar Kaduna.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An ce sun dura ofishin yakin neman zaben APC da ke titin NEPA, inda suke dauke da fastocin Sanata Shehu Sani tare da neman ya dawo APC.

Sanata Shehu Sani wanda ya wakilci Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa daga 2015 zuwa 2019 ya nemi takarar gwamnan Kaduna karkashin PDP 2023.

A cewar magoya bayan tsohon sanatan, suna da yakinin cewa Shehu Sani zai dawo cikin jam'iyya mai mulki a 'yan makonni masu zuwa.

An roki Sanata Shehu Sani ya bar PDP

Daya daga cikin jagororin wadanda suka sauya shekar kuma tsohon daraktan yakin neman zaben Sanata Shehu Sani a PRP, Monday Jaji ya yi karin haske.

Kara karanta wannan

Edo 2024: PDP ta fara korafi, dan takara ya fadi makircin da APC ta shirya

Mista Monday Jaji ya ce shekaru biyu kenan yana ta lallaba Shehu Sani a kan ya koma APC saboda nagartarsa da kuma aikin da ya yi lokacin ya na sanata.

Jaji ya ce Sanata Shehu Sani ya gina asibitoci bakwai a mazabarsa, ya raba na'urar raba wuta (tiransifoma) guda 200 tare da tallafawa mabukata da dama.

Da ya ke magana bayan karbar mutanen, shugaban APC na Kaduna, AC Emmanuel Jekada (mai ritaya) ya ce samunsu a tafiyar jam'iyyar zai kara mata nasara.

Shehu Sani ya yabi Uba Sani

A wani labarin, mun ruwaito cewa Sanata Shehu Sani ya tuno yadda suka yi gwagwarmayar '12 ga watan Yuni' a Najeriya inda har ya yabi gwamnan Kaduna, Uba Sani.

Tsohon sanatan na Kaduna ya kuma ce babu wata rawa da Malam Nasir El-Rufai ya taka a lokacin gwagwarmayar kwato 'yancin Najeriya sabanin ikirarin da tsohon gwamnan ya yi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.