Yanzu-yanzu: Shehu Sani ya janye daga takarar Sanata

Yanzu-yanzu: Shehu Sani ya janye daga takarar Sanata

Sanata Shehu Sani, mamba a majalisar dattijai daga jihar Kaduna, ya janye daga takarar neman jam'iyyar APC ta sake tsayar da shi takara a karo na biyu.

Sanata Sani, mai wakiltar Kaduna tsakiya a majalisar dattijai ta kasa, ya sanar da janye takararsa ne ta bakin mai taimaka masa a bangaren yada labarai, Abdulsamad Amadi, yau, Asabar a garin Kaduna.

"Muna masu sanar da ku al'umma cewar sanata Shehu Sani ba ya cikin zaben fitar da 'yan takarar sanatan Kaduna ta tsakiya dake gudana yanzu haka.

"Ofishin Sanata Shehu Sani bai tura ba, kuma ba zai taba tura wasu ba ko wani wakili ba wurin zaben da wasu jama'a suka shirya ba saboda uwar jam'iyyar APC ba ta kafa wani kwamiti domin ya gudanar da zaben ba a jihar Kaduna.

"A saboda haka duk wanda ya halarci taron, ya je ne don kashin kansa amma ba da yawun Sanata Shehu Sani ba.

Yanzu-yanzu: Shehu Sani ya janye daga takarar Sanata
Shehu Sani
Asali: Depositphotos

"Sanata Shehu Sani da magoya bayansa na biyayya ga doka, kuma zasu kasance masu biyayya ga tsari da hukuncin jam'iyya ko da yaushe," a jawabin Amadi.

A bangare daya kuma, a kalla daliget 3,200 ne yanzu haka ke can filin wasanni na Umaru Musa Yar'adua a garin Kaduna domin zaben dan takarar kujerar Sanatan Kaduna ta tsakiya a karkashin jam'iyyar APC.

Mutane 4 ne ke takarar neman APC ta tsayar da su takarar kujerar Sanatan Kaduna ta tsakiya, 'yan takarar su ne: Uba Sani, mai taimakawa gwamna El-Rufa'i a harkokin gwamnati, wani dan kasuwa, Usman Ibrahim da Shamsudden Giwa da kuma Sani Saleh.

DUBA WANNAN: An kara kashe wani sojan Najeriya a jihar Filato

Kazalika, Farfesa Edie Floyd-Igbo, shugaban gudanar da zabukan fitar da 'yan takara a jihar Kaduna da APC ta turo, ya bayyana cewar daliget 37 da suka fito daga mazabu 37 ne zasu kada kuri'a a zaben, bayan wasu daliget 5 da suka fito daga mazabun dake karkashin sanatoriyar Kaduna ta tsakiya.

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewar daliget daga kananan hukumomin Giwa, Kajuru, Chikun, Kaduna ta Arewa, Kaduna ta Kudu Birnin Gwari da Igabi ne zasu zabi dan takarar Sanata na yankinsu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng