KAI-TSAYE: Sakamakon Zaben Sabon Gwamna daga Kananan Hukumomin Edo

KAI-TSAYE: Sakamakon Zaben Sabon Gwamna daga Kananan Hukumomin Edo

A ranar Asabar aka fita kada kuri’u a zaben gwamnan jihar Edo inda za a san wa zai karbi mulki daga yanzu zuwa 2028.

Edo ta na da kananan hukumomi 18 da ke dauke da rumfunan zabe 4, 519. INEC ta tanadi na’urorin BVAS fiye da 5, 000.

Jami'ai sun kara tsaro a ofishin INEC

Jami’an tsaro sun cika ofishin hukumar INEC ana sauraron isowar zaben da aka tattara daga kananan hukumomin Edo.

Ana jiran isowar sakamakon zabe

Rahoton da aka samu daga tashar Channels ya ce a cikin kananan hukumomi 18, babu inda aka gama tara sakamako.

Babban kwamishinan INEC, Dr. Anugbum Onuoha ba zai iya fadi lokacin isowar kuri’un ba.

Sakamakon zabe sun hau IRev

Ana tattara sakamakon zaben gwamnan jihar Edo kuma rahotanni sun ce ana daura su a iRev domin duniya ta gani.

Punch ta ce sama da 90% na kuri'un da aka kada su na kan iRev da ke yanar gizo.

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng